
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Litinin Babbar Kotun Tarayya ta ɗaga sauraron shari’ar ƙarar da ke neman a dakatar da jagorancin tsagin su David Mark a jam’iyyar ADC daga ayyana kansu a matsayin jagororin jam’iyyar zuwa ranar 28 ga Satumba, 2026.
Rahotanni sun ce ƙarar, wadda fusataccen mamban ADC, Nafi’u Bala Gombe ya shigar, an sanya ranar sauraron ta ne tare da baki ɗaya ƙorafe-ƙorafen da aka gabatar wa Mai Shari’a Peter Lifu kan al’amarin. Saidai alƙalin bai samu halartar kotun ba, lamarin da ya sa aka gagar cigaba da gudanar da hukunci a kai. A saboda haka ne aka ɗage sauraron ƙarar, mai lamba FHC/ABJ/CS/1819/2025, zuwa ranar 28 ga Satumba.
A ranar 16 ga Yuni ne dai Mai Shari’a Lifu ya sanya lokacin sauraron ƙarar bayan yin watsi da ƙorafe-ƙorafe daban-daban da ADC da Sakatarenta na Ƙasa, Rauf Aregbesola suka shigar na a cire shi daga cikin shari’ar.
Akan haka ne alƙalin ya yi hukuncin cewa ƙorafe-ƙorafen nasu ba su da nagarta sannan ya kuma umarci ADC da Aregbesola su biya Naira miliyan 1 kowannensu ga Nafi’u Bala, matakin da ya sa suka zargi alƙalin da ɗaukar ɓangare da neman ya tsame hannunsa a shari’ar.
Shi dai Bala Gombe a ɓangarensa cikin korafin da ya shigar, ya buƙaci kotun da ta haramta wa Mark, Aregbesola da sauran mambobi Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa ayyana kawunansu a matsayin jagororin ADC, yana mai cewa zamansu a muƙaman ya saɓa wa dokokin ADC da na Zaɓe.
