
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta umarci a rufe Masallacin Juma’a na Sheikh Musa Lukuwa da ke Mabera a cikin garin Sakkwato bayan wani hari na kwanan nan da kisa da suka auku a masallacin.
Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnatin ta kuma kafa kwamitin malamai da za su yi bincike kan ababen da suka haddasa faruwar al’amarin da kuma bayar da shawarwarin da za su taimaka wajen kauce wa faruwar irin haka a nan gaba.
Masallacin, wanda gwamnatin jihar ta bayyana a matsayin “wurin laifi”, zai cigaba da kasancewa a rufe har illa ma sha Allahu, kamar yadda aka bayyana a wata takarda da Daraktan yaɗa labaran gwamnatin jihar, Abubakar Bawa ya fitar a ranar Talata.
Wannan na zuwa ne bayan fargabar lamuran addini acikin garin na Sakkwato, ciki har da kai wa Shehin malamin hari jim-kaɗan bayan kammala sallar Juma’a a masallacin.
Gwamnatin ta ce, kwamitin zai yi nazari kan abin da ya haifar da fargabar da bayar da shawarwarin da za su taimaka wajen tabbatar da zaman mai ɗorewa a jihar. Haka kuma, ta umarci a yi cikakken bincike kan harin da kisan wanda ya ƙaddamar da shi a masallacin.
Kazalika, gwamnatin ta barranta kanta da kowane mutum ba tare da la’akari da matsayi ba da yake fakewa da sunan addini wajen taɓa janibi ko munana ladabi akan fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW, kamar yadda kuma ta jaddada biyayyarta ga karantarwa da girmama shi tare da iyaye, iyalai da kuma sahabbansa, tana mai kira ga ‘yan jihar da su cigaba nuna soyayya da biyayya a gare shi (SAW).
A ƙarshe, ta buƙaci al’umma da su ƙaurace wa furta kalaman da ka iya tayar da zaune-tsaye musamman waɗanda za su haifar da rikici ga zaman lafiya a Sakkwato.
