
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Oludotun Baiyewu Jacobs, wato daɗaɗɗen jarumin nan na masana’antar shirya finafinan Nollywood da aka fi sani da Olu Jacobs ya rasu bayan shafe shekaru 84 a duniya. Ɗansa, Olusoji Jacobs ne ya sanar da labarin a yau Laraba, 16 ga Satumba, 2026.
Olusoji ya sanar rasuwar mahaifin nasa ne a wani saƙo da ya wallafa ta kafar Instagram, inda ya ce iyalansa na godiya bisa tsawon ransa da kuma roƙon al’umma da su girmama sirrinsu a wannan lokaci.
Olu Jacobs dai ɗaya ne daga cikin shahararrun jaruman finafinan Nijeriya wanda ya shafe tsawon lokaci yana aiki a harkar wasan kwaikwayo da gidajen talabijin da fim. Haka kuma, ya kasance shugaba a harkokin finafinai kuma jigo a ci-gaban masana’antar finafinan Nijeriya.
Marigayin jarumin ya kuma shahara da fitowa a matsayin mai faɗa-a-ji a finafinan Nijeriya da wasu ƙasashe, wanda ya sa ya zama jigo a tarihin fannin nishaɗantarwa a Nijeriya. Ya fito a finafinan da gidajen talabijin na Birtaniya suka shirya da finafinan ƙasa-da-ƙasa kafin zama babban jigo a masana’antar finafinai a Nijeriya.
A shekarun baya dai an yi ta yaɗa jita-jitar mutuwarsa a kafafen sada zumunta, duk da cewa iyalan nasa sun yi ta ƙoƙarin ƙaryatawa.
