Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Rundunar ‘yan sanda sun kama wasu da ake zargi ‘yan bindiga su da mai taimaka masu tare da cewo mutane biyu a Dutsinma da Kankia.
Sanarwa daga jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu,ya bayyana cewa yan sandan da suke gudanar da sintiri a hanyar ƙauyen Shema Fulani a ƙaramar hukumar Dutsinma suka suka kama mutane uku da ake zargi ‘yan bindiga ne bayan samun bayanan sirri.
Waɗanda ake zargi sun haɗa da Sani Dikko, Kabir Sani da Salisu Bello.
DSP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa a yayin da ‘yan sanda ke gudanar da bincike,wanda ake zargi Sani Dikko ya tabbatar da cewa shine da kan wasu mutane uku suka sace kakan sa wanda yake mahaifin babansa ne.
Wanda ake zargi ya ƙara da cewa kakan nasa sai da ya shafe kwanaki 16 a hannun su kafin su sako shi bayan sai da aka biya Naira miliyan uku a matsayin kuɗin fansa.
A Kankia kuwa yan sanda sun daƙile yunƙurin kai hari a ƙauyen shaiskawa Fulani na garin kankiya bayan da ‘yan bindiga su takwas suka sace mata biyu,Addini Rabe yar shekara 45 da Rabi Iyali yar shekara 27.
Sai dai bayan ɗauki ba daɗi da jami’an tsaro suka yi da yan bindigan,yan sanda sun sami nasarar ceto matan daga hannun yan bindigan.
DSP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa waɗanda ake zargi yanzu haka suna hannun jami’an ‘yan sanda a Katsina kuma da zaran an kammala bincike za a gurfanar da su a gaban kotu.
