Shugaban Afirka ta Kudu, Ramaphosa ya janye hada-hada bayan dawowa daga taron BRICS

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Cyril Ramaphosa na ƙasar Afirka ta Kudu ya janye daga shiga hada-hadar al’umma na wucin-gadi bayan dawowa daga taron jagororin ƙasashen BRICS a ƙasar Indiya, inda fadar shugaban ƙasar ta ce an ɗauki matakin ne sakamakon shawarar da likitocinsa suka bayar ta ya huce gajiya kafin koma wa harkokin mulki.

Fadar shugaban ƙasar ce ta sanar da wannan cigaba a wata takarda a ranar Laraba, 16 ga Satumba, 2026 ba tare da bayyana halin lafiyar shugaban ba mai shekaru 73.

A cewar sanarwar, Ramaphosa ya koma Afirka ta Kudu ne a ranar Litinin bayan shiga sahun jagororin da suka halarci taron BRICS karo na 18 a New Delhi, wanda daga bisani likitocinsa suka bada shawarar ya samu hutu kafin koma wa harkokin gwamnati.

Wannan al’amari na nufin Ramaphosa zai ja baya na wucin-gadi daga shiga harkokin jama’a duk da cewa babu wata alama mai nuna cewa ya damƙa ikonsa na mulki ga wani ko wata hukuma a ƙasar ko kuma hakan ya shafi harkokin gwamnatin ƙasar na yau da kullum.

Fadar ta bayyana cewa, shugaban ya kuma buƙaci ministoci da su wakilce shi a wasu harkokin yayin da yake halin karɓar kulawar likitoci duk da cewa ba a bayyana halin lafiyarsa ba ga al’umma.

Da fari dai fadar ta gargaɗi al’umma kan yaɗa labaran da ba a tantance su ba da suka shafi lafiyar manyan jami’an gwamnati da dogara da sanarwa da aka fitar a hukumance, tana mai cewa an dama da Shugaba Ramaphosa a zama daban-daban a taron na BRICS daga ranar 12 zuwa 13 ga Satumba.

By Babaji

Leave a Reply