Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Tsangayoyi 1,500 ne suka amince da shiga tsarin koyar da karatun boko da Gwamnatin Jihar Katsina ta ƙirƙira, inda aka fara koyar da ɗalibai darussan Turanci da Lissafi.
Shugaban Hukumar Ilimin Bai ɗaya ta Jihar Katsina, Dr Kabir Magaji Gafiya, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ofishinsa.
Ya ce tuni gwamnatin jihar ta ɗauki nauyin horar da malamai domin koyar da ɗalibai 3,000, tare da biyan waɗanda ke cikin shirin alawus na Naira 15,000.
Dr Kabir Gafiya ya bayyana cewa ɗaliban da shekarunsu suka ɗan haura za a ɗaga su zuwa ƙananan makarantun sakandare domin ci gaba da karatunsu.
Haka kuma, ya ce gwamnati ta samar da rumfuna tare da gina masu bandaki da samar da rijiyoyin burtsatse a kowace Tsangaya da ke cikin shirin.
Dr Gafiya ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta samar da kayan karatu da suka haɗa da littattafan rubutu, kujeru da allunan rubutu a Tsangayoyin.
“Suma malaman Tsangayar, gwamnati ta ba su horo tare da ba su kuɗaɗen gina rijiyar burtsatse a kowace Tsangaya,” inji Gafiya.
Ya yi kira ga shugabannin addini, sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki a harkar ilimi da su wayar da kan al’ummominsu kan muhimmancin shirin da Gwamnatin Katsina ta ƙirƙira, wanda a cewarsa zai bunƙasa harkokin ilimi a faɗin jihar.
Dr Kabir Gafiya ya kuma bayyana wasu ƙoƙarin da gwamnatin Katsina ta yi wajen bunƙasa ilimin yara, musamman masu buƙatu na musamman da waɗanda ke fama da wasu matsalolin lafiya.
Ya ce a kwanakin baya gwamnatin Katsina ta tallafa wa yara 5,750 da Naira 20,000 ga kowannensu, tare da raba wa ɗaliban makarantun firamare 12,625 littattafan karatu, jakunkuna, takalma da sauran kayan karatu domin ƙara musu ƙwarin gwiwa wajen neman ilimi.
