Daliban Arewa sun goyi bayan Tinubu a 2027

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugabannin ɗalibai daga manyan makarantu da ke jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya Abuja, sun bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

ɗaliban, waɗanda suka fito daga jami’o’i, kwalejojin kimiyya da fasaha da kuma kwalejojin ilimi, sun bayyana matsayinsu ne a ranar Talata yayin ƙaddamar da ɓangaren ɗalibai na ƙungiyar Arewa for Asiwaju (A4A).

Mai kula da ɓangaren daliban na A4A, Abdulmudallib Sheriff, wanda kuma shi ne Shugaban ƙungiyar Dalibai (SUG) ta Jami’ar Bayero da ke Kano, ya ce goyon bayan nasu ya samo asali ne daga matakan da gwamnatin Tinubu ta ɗauka a fannin ilimi, tallafin ɗalibai, koyar da sana’o’i da kuma bunƙasa matasa.

Sheriff ya ce ƙungiyar za ta fara gudanar da gangamin wayar da kan dalibai da neman goyon baya ga shugaban ƙasar a jami’o’i da sauran cibiyoyin ilimi.

Ya ce: “Muna tare da Asiwaju. Goyon bayanmu ba na baki kawai ba ne; tsari ne, an shirya shi kuma a shirye muke mu aiwatar da shi. Za mu kai wannan saƙo zuwa makarantu da al’ummominmu, mu wayar da kai, mu shirya tare da tattara mutane.”

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya danganta goyon bayan daliban da abin da ya kira manyan nasarorin gwamnatin Tinubu a fannonin ilimi, ababen more rayuwa, kiwon lafiya da noma.

By ukarofi

Leave a Reply