Har yanzu ana biyan basussukan Obi da Obiano – Soludo

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Jihar Anambra ta bayyana cewa har yanzu tana biyan wasu basussukan da gwamnatocin baya suka ci, ciki har da na tsoffin gwamnonin jihar, Peter Obi da Willie Obiano.

Kwamishinan Kuɗi na jihar, Izuchukwu Okafor, ne ya bayyana hakan ranar Lahadi yayin da yake magana a shirin Ndi Anambra Podcast, wanda tawagar New Media ta gwamnatin jihar ta fitar.

Okafor ya ce basussukan da aka gada na daga cikin manyan nauyin kuɗaɗen da gwamnatin yanzu ke fuskanta, yana mai cewa tun bayan da gwamnatin Chukwuma Soludo ta hau mulki, ba ta ci sabon bashin bankin kasuwanci ba.

Kwamishinan ya bayyana halin da kuɗaɗen jihar ke ciki da kuma matakan da gwamnatin Soludo ta ɗauka domin rage yawan basussukan da ake bin jihar, yana mai cewa gwamnati ta fi mayar da hankali wajen biyan basussukan da ake bi a baya maimakon ƙara cin sababbin basussuka.

Ya ce, “A rubuce yake cewa wannan gwamnati ba ta ci ko kwabo ɗaya na bashin bankin kasuwanci ba tun bayan da ta fara mulki.”

Sai dai Okafor ya bayyana cewa rashin cin sabon bashin banki ba yana nufin gwamnati ta daina biyan tsoffin basussuka ba, domin har yanzu ana cire wasu kuɗaɗen da ya kamata Jihar Anambra ta samu daga asusun tarayya domin biyan basussukan da gwamnatocin baya suka ci.

Kwamishinan ya danganta wasu daga cikin basussukan da ake biya a halin yanzu da gwamnatocin Peter Obi da Willie Obiano.

Ya ce, “An ci waɗannan basussuka ne a lokacin Peter Obi da Willie Obiano, tsoffin gwamnonin jihar.”

Peter Obi, wanda ke takarar shugaban ƙasar Nijeriya a ƙarƙashin jam’iyyar Nigeria Democratic Congress, ya sha bayyana cewa ya inganta Jihar Anambra tare da barin makudan kuɗaɗe a taskar jihar a lokacin da ya bar mulki.

Sai dai wannan iƙirari ya sha fuskantar suka daga magajinsa, Chukwuma Soludo, wanda ya ci gaba da ƙalubalantar iƙirarin Obi kan yanayin kuɗaɗen jihar da ya gada.

By ukarofi

Leave a Reply