Matasan ‘yan wasan ƙwallon kafa su huɗu daga ƙaramar hukumar Ɓatagarawa sun samu dama ta musamman da za ta iya buɗe musu ƙofofin buga ƙwallo a matakai daban-daban, ciki har da ƙasashen waje.
An zaɓi matasan ne a ranar farko ta Galadima scouting program 2026, wani shiri da aka shirya domin zaƙulo matasan ‘yan wasa masu hazaƙa da baiwa.
Shirin ya gudana ƙarƙashin jagorancin Mr. Aljosa Alebegovic, wakilin ‘yan wasan ƙwallon kafa mai lasisin FIFA, tare da Mr. Datty, inda suka gudanar da atisayen tantancewa da zaɓen matasan da suka nuna ƙwarewa da ƙwazo.
Matasan da suka samu wannan dama sun haɗa da Almustafa Usman da Muhammad Lurwan sai Abdulrahman Muhammad da kuma Paul Oviosun
Shirin na da nufin samar da damammaki ga matasan ‘yan wasan Katsina domin su ci gaba da haɓaka ƙwarewarsu tare da samun damar shiga manyan matakan ƙwallon ƙafa a gida da ƙasashen waje.
Yanzu haka akwai wasu yan wasan ƙwallon ƙafa daga Jihar Katsina da ke buga tamola a wata ƙungiya na ƙasar Belarus.
