Neja: An sanya dokar ta-ɓaci a Minna yayin zanga-zangar mutuwar masu haƙar ma’adinai 37

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago ya ayyana dokar kulle ta kwana guda a sassan Minna sakamakon zanga-zanga da ta ɓarke a birnin kan mutuwar wasu da ake zargin ‘yan haƙar ma’adinai ne su 37 a ofishin Hukumar Sibil Difens (NSCDC) a jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa, dokar ta fara aiki ne yayin da aka kammala sallar Juma’a kuma za ta cigaba da aiki har illa ma sha Allahu. A saboda haka ne aka shawarci mazauna da su cigaba da zama a cikin gidajensu da guje wa zirga-zirga mara muhimmanci yayin lokacin kullen.

Sannan, an shawarci hukumomin tsaro da su tabbatar da al’umma sun yi biyayya ga dokar yayin da suke ƙoƙarin bayar da kariya ga rayuka da dukiyoyinsu acikin babban birnin jihar.

Hakan na zuwa ne kwana guda da aka samu labarin rasuwar masu haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba guda 37 a ofishin hukumar Sibil Difens (NSCDC) reshen Neja, inda daga bisani Gwamnatin Tarayya ta dakatar da kwamandan NSCDC na jihar.

Haka kuma, gwamnatin Neja ta kafa kwamitin binciken domin gano ainihin abin da ya sabbaba mace-macen. Wannan al’amari dai ya haddasa cece-kuce a faɗin Nijeriya inda mahukunta suke kira da a kwantar da hankali yayin da ake gudanar da bincike a kai.

By Babaji

Leave a Reply