Mutuwar mutane 37 a tsare: Sarkin Hausawan Tukulma ya nemi a binciki NSCDC

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

Shugaban ƙungiyar Arewar mu duniyar mu African chiefdom and council, kuma Sarkin Hausawan Tukulma a Jihar Gombe, Ambasada Alhaji Ibrahim Haruna, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da cikakken bincike kan mutuwar mutane 37 da suka mutu a hannun jami’an hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC) a Jihar Neja.

Ambasada Ibrahim ya bayyana lamarin a matsayin abin da ke buƙatar a gano gaskiyar abin da ya faru, musamman ganin cewa waɗanda suka mutu na daga cikin mutanen da aka kama bisa zargin gudanar da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.

Ya ce rahotannin farko sun bayyana mutuwar mutane 33, kafin daga bisani adadin ya tashi zuwa 37, yayin da hukumomi ke ci gaba da bincike domin gano ainihin musabbabin mutuwar.

Ya buƙaci a gudanar da bincike mai zaman kansa, cikin gaggawa da gaskiya, domin tantance yadda mutanen suka mutu da kuma ko akwai wani sakaci ko take haƙƙin ɗan Adam da ya faru yayin da suke tsare.

“Wannan kira ba na zargi ba ne, kuma ba na tayar da hankali ba ne. Kira ne na adalci, gaskiya, bin doka da kare rayukan al’umma,” in ji shi.

Sarkin Hausawan Tukulma ya ce ya kamata binciken ya duba yanayin wurin da ake tsare da mutanen, tsawon lokacin da suka yi a wurin, irin kulawar da aka ba su da kuma ko sun samu isasshen abinci, iska da kulawar lafiya.

Ya kuma buƙaci a gudanar da cikakken binciken likitanci tare da gudanar da gwaje-gwajen da suka dace, domin gano ainihin musabbabin mutuwar kafin a yanke hukunci kan lamarin.

Kiran nasa ya zo ne yayin da hukumomi a Neja suka kafa kwamitin bincike kan mutuwar mutanen, yayin da kuma aka dakatar da Kwamandan NSCDC na Jihar Neja, Suberu Siyaka Aniviye, domin gudanar da bincike kan lamarin.

Ambasada Ibrahim ya kuma buƙaci a bai wa iyalan waɗanda suka mutu cikakken bayani kan abin da ya faru da ’yan uwansu, tare da tabbatar da cewa duk wani jami’i da bincike ya nuna yana da hannu wajen take doka zai fuskanci hukuncin da doka ta tanada.

Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakan da suka dace domin hana sake faruwar irin wannan lamari, musamman ta hanyar tabbatar da bin ƙa’idojin tsare mutane da kare haƙƙin su.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, su guji ɗaukar doka a hannunsu, sannan su bai wa hukumomin da suka dace damar gudanar da bincike cikin gaskiya da adalci.

A ƙarshe, Sarkin Hausawan Tukulma ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasu, ya bai wa iyalansu haƙuri, Ya kuma tabbatar da adalci da zaman lafiya a Jihar Neja da Najeriya baki ɗaya.

By ukarofi

Leave a Reply