Zaɓe: ADC ta buƙaci INEC ta daina amfani da malaman jami’a masu ra’ayin siyasa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar ADC ta buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta sake duba amfani da malaman jami’a masu ra’ayin siyasa a matsayin jami’an tattarawa da haɗa sakamakon zaɓe a 2027.

Kiran ya biyo bayan rahoton cewa sama da manyan malaman jami’o’in gwamnati 600 daga Arewacin Nijeriya sun nuna goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027.

A cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya fitar, jam’iyyar ta ce duk da ’yancin malaman jami’a na goyon bayan dan takarar da suke so, bai kamata a ba wanda ya bayyana ɓangaren da yake goyon baya aikin tantancewa da bayyana sakamakon zaɓen da ɗan takarar ke ciki ba.

ADC ta buƙaci INEC ta kafa ka’idojin da za su hana mutanen da suka fito fili suka goyi bayan ’yan takara ko suka shiga harkokin siyasa zama jami’an zaɓe.

Haka kuma, ta nemi INEC ta wallafa sunayen jami’an tattara sakamakon da za a nada tun kafin zaɓe, domin jam’iyyun siyasa da jama’a su samu damar nuna duk wani rikici na moriya.

By ukarofi

Leave a Reply