’Ya’yana sun isa su gaji kasuwancina duk da mata ne – Dangote

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa samun ɗa namiji da zai gaji daular kasuwancinsa ba shi ne babban abin da ya fi ba shi muhimmanci ba, yana mai cewa ’ya’yansa mata uku suna da cikakkiyar damar jagorantar Rukunin Kamfanonin Dangote nan gaba.

Dangote ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na ARISE a ranar Talata, inda ya ce yana ganin ɗaya daga cikin ’ya’yansa mata na iya zama jagorar babbar daular kasuwancin iyalin. Da aka tambaye shi ko yana ganin ɗaya daga cikin ’ya’yansa mata za ta iya karɓar ragamar jagorancin kamfanin, Dangote ya ce yana ganin hakan zai yiwu, domin ya daɗe yana lura da irin ƙwazon kowannensu.

’Ya’yan Dangote mata, Halima, Fatima da Mariya, suna riƙe da manyan muƙamai a cikin rukunin kamfanonin, yayin da nauyin da ke kansu ke ƙaruwa a daidai lokacin da kamfanin ke tsara yadda za a miƙa ragamar shugabanci nan gaba.

Dangote ya ce, shiga harkokin kasuwancin iyali da ’ya’yansa mata suka yi ba sakamakon matsin lamba daga gare shi ba ne, sai dai saboda sha’awarsu da kansu. Ya ce ’ya’yansa mata suna da matuƙar sha’awar kasuwancin, kuma suna jin daɗin aikin da suke yi, yana mai cewa ba ya tilasta musu shiga harkokin kamfanin.

Attajirin, wanda shi ne ɗaya daga cikin fitattun ’yan kasuwa a Afirka, ya ce yana da yaƙinin cewa ’ya’yansa mata na iya zarce irin nasarorin da ya samu tare da ɗaga kamfanin zuwa wani sabon matsayi. A cewarsa, kasancewarsu masu ilimi sosai zai taimaka musu wajen samar da sabbin dabaru da hanyoyin bunƙasa kamfanin fiye da yadda yake a yanzu.

Da aka tambaye shi ko yana ganin dukkansu ukun suna da wannan ƙwarewar, Dangote ya amsa da cewa: “Dukkansu.”

Da aka tambaye shi ko har yanzu yana fatan samun ɗa namiji, musamman ganin yadda al’adun al’ummar Kano ke bai wa ɗa namiji muhimmiyar rawa wajen gadon dukiyar iyali, Dangote ya ce wannan ba shi ne abin da ya fi damunsa ba. Ya ce, samun ɗa namiji ba lallai ne ya zama tabbacin ci gaba da ɗaukakar sunan iyali ba, domin mutum ba zai iya sanin irin rayuwar da ɗan da zai haifa zai yi a nan gaba ba.

Dangote ya ce wani lokaci mutum kan yi addu’ar Allah Ya ba shi ɗa namiji, amma ɗan na iya zama wanda zai jawo koma baya ga martabar iyali. Ya ƙara da cewa, idan Allah bai ba mutum wani abu ba, bai kamata ya matsa wajen neman hakan ta kowace hanya ba, yana mai cewa bai yi imanin ɗa namiji zai yi abin da ya fi abin da ’ya’yansa mata uku suka iya yi ba. “Ba na ganin samun ɗa namiji shi ne fifikona,” inji shi.

Dangote ya bayyana cewa shirinsa na rabon ragamar kamfanin a nan gaba bai ta’allaƙa kawai kan miƙa shugabanci ga wani ɗan iyali ba, illa tabbatar da cewa kamfanin yana ƙarƙashin ingantaccen tsarin gudanarwa na ƙwararru. Ya ce, burinsa shi ne a gudanar da kamfanin bisa ƙa’idojin ƙwarewa tare da samar da ingantaccen tsarin sa ido da shugabanci na kamfani.

Dangote ya kawo misalan manyan kamfanonin duniya irin su Microsoft da Apple, waɗanda suka ci gaba da bunƙasa duk da cewa waɗanda suka kafa su ba sa jagorantar kamfanonin a yau. Ya ce, suna son samar da tsarin da zai yi matuƙar wahala ga duk wani ɗan iyali ya samu damar lalata nasarorin da aka gina cikin shekaru.

Yayin da yake magana kan abin da yake son a tuna da shi da shi bayan rasuwarsa, Dangote ya ce babban burinsa shi ne bayar da gagarumar gudunmawa wajen mayar da Afirka nahiyar masana’antu.

Ya ce ba zai iya cimma wannan buri shi kaɗai ba, amma yana da cikakken yaƙinin cewa a cikin shekaru biyu ko uku masu zuwa, wasu ’yan Afirka za su haɗa kai da shi wajen ganin an cimma wannan buri.

By ukarofi

Leave a Reply