Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Jigo a jam’iyyar All Progressives Congress, APC, kuma mai neman kujerar Sanata a Zamfara ta Arewa, Dr. Sani Abdullahi Shinkafi, ya zargi hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, da ƙin bin umarnin kotu na soke zaɓen fidda gwani na Sanata a Zamfara ta Arewa.
Shinkafi ya yi Allah wadai da buga sunan Sanata Sahabi Alhaji Ya’u a matsayin ɗan takarar jam’iyyar a Zamfara ta Arewa, yana mai bayyana hakan a matsayin karya umarnin babbar kotun tarayya da ke Gusau.
Shinkafi a cikin wata sanarwa yau Asabar ya ce, babbar kotun tarayya, zashen shari’a a Gusau, a cikin ƙara mai lamba FHC/GS/CS/6/2026 da aka gabatar a ranar 31 ga Agusta, 2026, alƙali Hassan Dikko ya soke zaɓen fidda gwani na Sanatan APC a Zamfara ta Arewa da aka gudanar a ranar 19 ga Mayu, 2026.
Kotun, a cewarsa, ta yanke hukuncin cewa ba a bi tsarin da ya dace ba, tare da tsawatarwa cewar zaɓen ya saɓa wa dokar zaɓe ta 2026 da ƙa’idojin jam’iyya, kuma babu wani ɗan takara mai inganci a yankin.
Bayan haka, kotun ta umarci APC ta gudanar da sabon zaɓen fidda gwanin Sanata a Zamfara ta Arewa cikin kwanaki 14, bayan hukuncin kuma ta umarci INEC da ta amince da sakamakon.
Shinkafi ya bayyana cewa hukumar ta INEC tana cikin waɗanda yake ƙara a gaban kotun, kuma an ba ta takardar shaidar hukuncin don bin ƙa’ida.
“Bai dace ba, rashin adalci ne aka haɗa kuma cin zarafi ne ga dimokuraɗiyya mai tasowa a ƙasar nan, INEC ta karya umarnin kotu mai iko,” in ji Shinkafi.
Ya yi jayayya cewa wallafa sunan kowane ɗan takara kafin sabon zaɓen fidda gwani da kotu ta umarta ko kuma kafin a yanke hukunci a kotun ɗaukaka ƙara ya ɓata shari’a a matsayin wurin shari’a da kuma muradi na ƙarshe na ‘yan ƙasa da suka fusata.
“A matsayina na ɗan takarar da ke ƙara a gaban kotu, hukumar zaɓe INEC ya kamata ta kare sahihanci da amincin tsarin zaɓe, gami da jam’iyyun siyasa, da hanyoyin zaɓe”.
“Rashin bin umarnin kotu a cikin al’amarin da hukumar zaɓen zai ɓata amincewar jama’a ga tsarin zaɓen da ke tafe a yankin Zamfara ta Arewa” in ji shi.
Jigon APC ya yi gargaɗin cewa irin wannan rashin biyayya ga kotu yana raunana dimokuraɗiyya kuma yana karya dokokin zaɓe.
Ya jaddada cewa dole ne INEC ta bi ingantattun hukunce-hukuncen kotu don gina amincewar jama’a da kuma tabbatar da mutuncin dimokuraɗiyya kafin babban zaɓen 2027.
Dr. Sani Abdullahi Shinkarfi hakazalika ya buƙaci a janye sunan Sanata Sahabi Alhaji Ya’u nan take a matsayin ɗan takarar gundumar Sanata ta Zamfara ta Arewa.
