2027: ADC ta buƙaci masu zaɓe su kare ƙuri’unsu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta yi kira ga masu zaɓe da su guji sayar da kuri’unsu, tare da kare su daga duk wani nau’in magudi a zaɓen shekarar 2027.

Jam’iyyar ta yi wannan kiran ne a yayin da take gabatar da ’yan takararta a mazabar Sanata ta Daura, waɗanda za su fafata a zaɓen 2027.

An gabatar da ’yan takarar ne a hedikwatar jam’iyyar da ke TBO Kwanar Dabo a Daura, inda shugabannin jam’iyyar, ’yan takara da magoya baya daga sassa daban-daban na jihar suka halarta.

Wakilin jam’iyyar a wajen taron, Mataimakin ɗan takarar Gwamnan Katsina, Akitet Aminu Yar’Adua, ya gabatar da Honorabul Sani Lawal Garki, mai wakiltar mazabar tarayya ta Baure/Zango a Majalisar Wakilai, a matsayin ɗan takarar jam’iyyar na kujerar Sanata mai wakiltar Daura.

An kuma gabatar da sauran ’yan takarar jam’iyyar na Majalisar Wakilai da Majalisar Dokokin Jihar Katsina, waɗanda za su fafata a mazabu daban-daban na yankin.

Da yake jawabi ga mahalarta taron, Garki ya buƙaci matasa da sauran masu zaɓe da su yi watsi da yunƙurin wasu ’yan siyasa na sayen kuri’u.

Ya ce ya kamata masu zaɓe su yi amfani da kuri’unsu wajen neman shugabannin da za su riƙa bayyana wa jama’a yadda suke tafiyar da mulki, tare da yin aiki wajen inganta rayuwar al’umma.

Ya kuma buƙaci jama’a da su zaɓi ’yan takarar da za su iya magance matsalolin tsaro, tsadar rayuwa da sauran ƙalubalen da ke addabar al’umma.

“Kar ku sayar da makomarku saboda kuɗi. Kuri’arku ce ƙarfin ku, don haka ku kare ta,” in ji Garki, yayin da ya buƙaci masu zaɓe da su kasance cikin taka-tsantsan a dukkan matakan zaɓe.

A saƙon fatan alheri a madadin ’yan takarar Majalisar Wakilai da Majalisar Dokokin jihar, ɗan takarar ADC na mazabar Daura/Sandamu/Mai’Adua, Injiniya Abdul Rashid Nasir, ya bayyana taron a matsayin muhimmin mataki wajen ƙarfafa haɗin kai da faɗaɗa tsarin jam’iyyar a matakin ƙasa.

Daga cikin mahalarta taron har da Babangida Talau Malumfashi, Shugabar Mata ta ADC a Katsina, Hajiya Amina Lawal; Birgediya Janar Maharazu Tsiga; da Alhaji Lawal Batagarawa.

Shugabannin jam’iyyar sun ce za su ci gaba da aiki tare da ’yan takara, magoya baya da sauran masu ruwa da tsaki domin ƙarfafa tsarin jam’iyyar a faɗin jihar gabanin zaɓen 2027.

By ukarofi

Leave a Reply