Sanata Barau ya sallami mataimaki kan wallafa “Abba Must Go” yayin da APC da Kwankwaso ke fafutukar nasara a Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ya kori mai taimaka masa na musamman kan harkokin majalisa, Umar Alhassan da aka fi sani da King Indara sakamakon wallafe-wallafe akan Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano.

Wannan mataki ya fara aiki ne a ranar Juma’a, 18 ga Satumba, 2026, a cewar wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran Sanata Barau, Shitu Madaki Ƙunchi ya fitar. Sanatan ya ce ya ɗauki wannan mataki ne bisa abin da ya kira da “rashin girmamawa” daga mataimakinsa a Soshiyal Mediya.

Musamman sanarwar ta kawo misali da wallafar Indara ta “Abba Must Go”, wanda sanatan ya bayyana a matsayin abin da ya bai dace ba jami’an ofishinsa su siffanta da shi. Ya kuma ce hakan ba ɗabi’a ba ce ta ‘ya’yan jam’iyyar APC ko kuma dokoki da sharuɗɗanta.

Sanatan Kanon ta Arewa ya kuma jaddada ƙoƙarinsa ga APC da kuma nuna fatan kai ta ga nasara “daga sama har ƙasa” a yayin babban zaɓen 2027.

Gabanin sallamar, Indara, wanda ɗan TikTok ne mazaunin Kano, ya kuma yi wata wallafa a ranar Juma’ar, inda a ciki ya rubuta cewa Kano ta Kwankwaso ce, amma kuma har yanzu shi ɗan APC ne.

By Babaji

Leave a Reply