Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), reshen Jihar Katsina, ta gudanar da addu’ar neman zaman lafiya da ci gaban Najeriya, tare da roƙon Allah ya kawo ƙarshen matsalolin tsaro da sauran ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.
A cewar wata sanarwa da Abubakar Ahmed, jami’in hulɗa da jama’a na yaƙin neman zaɓen ɗan takarar gwamnan jihar Katsina na jam’iyyar ADC, Sanata Ahmad Babba Kaita, ya fitar, an gudanar da taron ne a ofishin ɗan takarar da ke Katsina.
Sanarwar ta ce mahaddata alƙur’ani sun gudanar da karatun littafin mai tsarki tun daga safiya zuwa lokacin La’asar, kafin a gudanar da sallar La’asar da addu’o’i.
An mayar da addu’o’in kan neman ƙarshen rashin tsaro, ta’addanci, talauci, yunwa, cututtuka, cin hanci da rashawa da sauran matsalolin da ke addabar al’umma.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban masu shirya taron, Hon. Abdurrazak Kaita, ya ce an shirya taron ne domin neman mafita daga ƙalubalen da al’umma ke fuskanta, musamman rashin tsaro da matsin tattalin arziki.
Mahalarta taron sun kuma roƙi Allah ya tona asirin masu taimaka wa ’yan ta’adda, tare da kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci da sauran laifukan da ke cutar da al’umma.
Sanarwar ta ƙara da cewa an yi addu’ar Allah ya ƙara wa Sanata Ahmad Babba Kaita lafiya yayin da yake ci gaba da samun sauƙi daga jinya, tare da yi masa fatan dawowa cikin ƙoshin lafiya.
Haka kuma, an roƙi Allah ya ba ’yan takarar jam’iyyar ADC nasara a zaɓe mai zuwa, tare da ba su ikon gudanar da amanar da za a ba su.
Taron ya samu halartar malamai, mata, shugabannin al’umma da ɗaruruwan ya’yan jam’iyyar ADC.
ADC ta gudanar da addu’ar neman zaman lafiya a Katsina
