ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Mai baiwa Gwamnan Jihar Katsina shawara kan harkokin cigaban al’umma, Alhaji Abubakar Tsanni, ya ajiye muƙamin sa.
Kamar yadda jaridar Katsina Times ta ruwaito ofishin sakataren gwamnatin Jihar Katsina ta sami tabbacin haka.
A cewar kafar yaɗa labaran, Alhaji Abubakar Tsanni ya rubuta takardar ajiye mukaminsa ne a ranar 22 ga watan Satumba, 2026, inda ya bayyana godiyarsa ga Gwamnan Jihar Katsina bisa damar da ya ba shi ta yin aiki a cikin gwamnatinsa.
A cikin takardar, Tsanni ya bayyana cewa zai ci gaba da nuna godiya da girmamawa ga gwamnatin Gwamnan Katsina bisa damar da aka ba shi na yi wa al’umma hidima a cikin gwamnatin.
A halin yanzu, Alhaji Abubakar Tsanni na shugabantar wasu ƙungiyoyi da dama da ke gudanar da ayyukan wayar da kan jama’a da neman sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Dikko Umar Raɗɗa.
Daga cikin kungiyoyin da yake jagoranta akwai A4A – Arewa for Asiwaju, da kuma GMTD.
