Shugaban hukumar yaƙi da zaizayar ƙasa na Jihar Katsina ya ajiye aikinsa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban hukumar yaƙi da zaizayar ƙasa na jihar Katsina, Barrister Sulaiman Muhammad Namadi, ya ajiye muƙamin sa.

Wannan kuwa na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban hukumar ya fitar, domin bayyana wannan mataki da ya ɗauka.

Barrister Sulaiman Namadi ya gode wa Gwamna Dikko Raɗɗa bisa damar da ya ba shi ta yin aiki domin cigaban jihar Katsina.

Haka zalika ya yi wa Gwamnan da Jam’iyyar APC fatan samun nasara.

Wannan dai na zuwa ne kwana guda kacal, bayan da mai baiwa Gwamnan Jihar Katsina shawara a kan cigaban al’umma, Alhaji Abubakar Tsanni ya ajiye muƙamin sa, lamarin da ya jawo tattaunawa da bayyana mabanbantan ra’ayoyi a kafafen sada zumunta.

By ukarofi

Leave a Reply