Dalilin kotu na soke tikitin takarar Pantami

Spread the love

*Ta umarci PDP ta sake gudanar da zaɓen fidda gwani

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babbar Kotun Tarayya da ke zaman ta a Gombe, Babban Birnin Jihar Gombe, ta umarci babbar jam’iyyar adawa a jihar, wato PDP da ta sake gudanar da sabon zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar, domin tabbatar da tantance ɗan takararta na gwamnan jihar ta Gombe.

Mai Shari’a Amina Aliyu Mohammed ce ta bayar da umarnin a jiya Alhamis bayan sauraron ƙarar da Usman Aliyu Garry ya shigar yana mai ƙalubalantar tsayar da Farfesa Isa Ali Pantami a matsayin ɗan takarar jam’iyyar na gwamna.

Usman Garry ya ƙalubalanci tsayar da Sheikh Pantami ne bayan da PDP ta sanar da shi a matsayin ɗan takararta tilo a ranar 26 ga Yuni, 2026, yana mai cewa, ba a gudanar da zaɓen fitar da gwani, kamr yadda ya dace a yi a jihar na jam’iyyar ba.

Farfesa Pantami, wanda tsohon mai neman takarar gwamna a Jam’iyyar APC ne, ya koma PDP ne bayan APC ta tsayar da Jamilu Gwamna a matsayin ɗan takararta na yarjejeniya a zaɓen da za a gudanar na 2027.

Daga bisani, Pantami, wanda malamin addini ne, ya ƙi amincewa da tsarin masalahar da APC ta aiwatar, lamarin dsa ya sanya ya samu tikitin PDP ta hanyar amincewa da fatar baki yayin zaɓen fitar da gwani da jam’iyyar ta gudanar a watan Mayu, zaɓen da aka riƙa kallo shi ma a matsayin na masalaha ne irin wanda farfesan ya ƙi amincewa da shi a APC.

Sai dai kotun, a hukuncin da ta yanke ranar Alhamis, ta umarci PDP da ta sake gudanar da zaɓen fidda gwani bisa ƙa’idojin jam’iyyar da kuma tanade-tanaden dokokin zaɓe.

By ukarofi

Leave a Reply