Nijeriya da Amurka sun ƙulla yarjejeniyar bunƙasa haƙo ma’adinai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya da ƙasar Amurka sun rattaɓa hannu akan yarjejeniyar ƙarfafa matakin zuba jarin Amurka a fannin haƙar ma’adinan Nijeriya da tafiyar da ci-gaban albarkatun ƙasa a Nijeriya.

Ministan Ci-gaban Albarkatun Ƙasa, Dele Alake ne ya sanya hannu a yarjejeniyar a madadin gwamnatin tarayya yayin da Mataimakin Sakataren Gwamnatin Amurka, Christopher Landau ya wakilci Amurka a ɗaya gefen, a Nigeria House da ke New York a wani ɓangare na babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 81.

Alake ne ya sanar da wannan ci-gaba ne ta kafar X a ranar Alhamis, inda ya ce tsarin zai shafi bayanan faɗin ƙasa da girman matakin da za a shiga, ci-gaban albarkatun ƙasa da hanyoyin samarwa, ababen more rayuwa da ƙarfin fasaha. A cewarsa, gwamnati tana ƙiyasta arziƙin albarkatun ƙasar Nijeriya a kusan Dala biliyan 700.

Haka kuma ya ce, Nijeriya ba za ta cigaba da zama a matsayin mai samar da ɗanyen albarkatu ba yayin da wasu ke amfani da ainihin darajarsu, saidai, tana buƙatar samarwa a matakin gida, nagartattun ayyukan yi, ƙarfin ƙwarewa a fannoni daban-daban da damarmakin ga sana’o’in Nijeriya.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Nijeriya take ƙoƙarin janyo ra’ayoyin masu zuba jari daga waje a fannin albarkatun ƙasa da ƙara ɗaga darajarta a idon duniya.

By Babaji

Leave a Reply