Taron UNGA 81: Shettima ya nema wa shirin Sabuwar Nijeriya goyon bayan ‘yan ƙasa mazauna waje

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya kirayi ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje musamman masu zama a Amurka da su bai wa Shirin Ajandar Sabunta Fata ta gwamnatin Shugaba Bola Tinubu goyon baya wajen bunƙasa nasarorin tattalin arziƙin ƙasar.

Shettima ya yi wannan magiya ne a wata ganawa da su yayin wani taro da Shugaban NIDCOM, Hon. Abide Dabiri Erewa ya shirya, wanda aka gudanar a Nigeria House da ke Birnin New York.

Mataimakin Shugaban ƙasar ya ce gwamnatin Shugaba Tinubu tana iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta daidaita lamuran tattali musamman kan fannonin ilimi, lafiya, kimiyya da fasaha, noma da kuma ƙoƙarin amfani da ilimin ‘yan ƙasar mazauna waje wajen bayar da gagarumar gudunmawa ga goben Nijeriya.

Shettima ya kuma ce, Shugaba Tinubu ya kasance cikin yaƙini tun daga farkon mulkinsu wajen ɗaukar matakai masu tsauri da ke taimaka wa daidaita lamuran tattali a Nijeriya, yana mai cewa hakan ya sa an samu kyawawan sakamako musamman akan ƙara adadin kuɗaɗen ajiyar ƙasar a ƙasashen waje daga Dala biliyan 3.9 zuwa sama da Dala biliyan 55, wanda ke nuna ƙarin kaso 4.45.

Ya ƙara da cewa, gwamnatin ta kashe jimillar Naira biliyan 125 a Shirin Asusun Bayar da Lamunin karatu, inda ɗalibai 1.29 suka amfani da shirin tun bayan kafa shi. Don haka ya yi kira a gare su da su kasance masu ƙoƙarin taimaka wa ƙasar wajen samun nasarori ta hanyar dunƙulewa waje guda domin tabbatar da hakan.

Taron ya samu halartar gwamnonin jihohin Borno, Babagana Zulum; Abdulrahman AbdulRazaq na Kwara; Siminalayi Fubara na Ribas; Dauda Lawal na Zamfara; Jagoran Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, da matan gwamnonin jihohin Kwara, Katsina, Abia da Osun.

Sauran sun haɗa da ministocin Harkokin Waje, Amb. Bianca Odumegwu-Ojukwu; Kimiyya, Fasaha da Ƙirƙira, Dakta Kingsley Tochukwu Udeh; Jin-ƙai da Rage Talauci, Dr Bernard Doro; Ilimi, Dakta Tunji Alausa; Ci-gaban Albarkatun Ƙasa, Cif Dele Alake; Harkokin Mata, Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim, Ƙaramar Minister Kasafi da Shirin Tattali, Dakta Doris Uzoka-Anite; Ƙaramar Ministar Abuja, Dakta Mariya Bunkure, Babban Wakilin Nijeriya ga Majalisar Ɗinkin Duniya, Amb. Jimoh Ibrahim; Jakadan Nijeriya ga Washington, Amb. Kayode Are, da wasu jagororin hukumomin gwamnati da manyan jami’an gwamnati.

By Babaji

Leave a Reply