2027: Atiku ya naɗa El-Rufa’i cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC duk da yana tsare

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, ya sanya tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai acikin tawagar kwamitin yaƙin neman zaɓensa na shugaban ƙasa a 2027.

Rahotanni sun bayyana cewa, ɗan takara shugaban ƙasar a jam’iyyar ADC, ya sanar da naɗin El-Rufa’i ne a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis. Wannan naɗi ɓangare ne na bayyana tsarin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar.

A halin yanzu dai El-Rufa’i yana tsare a hannun Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC), inda yake fuskantar tuhume-tuhume masu alaƙa da rashawa. Yana fuskantar tuhume-tuhume ne da suka haɗa da waɗanda Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Kaduna suka shigar da shi ƙara akansu.

Saidai, tsohon gwamnan ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa, yana mai iƙirarin gurfanarwa da ake masa na da alaƙa da siyasa. Tun a watan Fabarairu ne dai aka tsare tsohon gwamnan. ICPC dai ta ce ta cigaba da tsare shi ne bisa umarnin kotu.

By Babaji

Leave a Reply