Shugabanni da masana sun yaba da shirin HUNEXPO2 kan Hajji da Umara

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Shugabanni, malamai, masana da sauran masu ruwa da tsaki sun bayyana gamsuwarsu kan wani taron wayar da kai da aka shirya domin tattauna hanyoyin inganta tafiye-tafiyen aikin Hajji da Umara da sauran tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje, tare da duba yadda za a yi amfani da irin waɗannan tafiye-tafiye wajen bunƙasa tattalin arzikin al’umma da ƙasa baki ɗaya.

An gudanar da taron ne a matsayin taro na biyu a tarihin cibiyar HUNEXPO, wanda aka shirya ƙarƙashin jagorancin Dakta Aisha Ahmad. Taron ya ɗauki yini ɗaya kuma an gudanar da shi a birnin Kano a makon da ya gabata.

Da yake jawabi a taron, Hon. Muhammad Chiroma na Laraba, ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Gezawa da Gabasawa a Jihar Kano, kuma mataimakin shugaban kwamitin kula da aikin Hajji a Majalisar Wakilai ta Tarayya, ya bayyana muhimmancin irin wannan taro wajen wayar da kan jama’a da inganta harkokin tafiye-tafiyen addini.

Shi ma tsohon shugaban Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Usman Saleh Pakistan, ya bayyana cewa irin wannan taro yana da matuƙar muhimmanci, saboda harkar aikin Hajji da Umara na buƙatar samun ilimi da shiri a kai a kai.

Ya ce ya zama dole masu ruwa da tsaki su riƙa sabunta iliminsu saboda yadda abubuwa ke sauyawa cikin sauri a wannan zamani, tare da yin tanadi da shiri yadda ya kamata.

Ya ce hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki a harkar aikin Hajji da Umara, da kuma sauran tafiye-tafiye na addini, neman ilimi da bunƙasa tattalin arziki, ya kamata su gudanar da ayyukansu bisa tsarin doka.

Haka shi ma shugaban kula da dabarun zuba hannun jari na Jihar Yobe, Dakta Aliyu Isah Cikaji, ya ce duk wani shiri da zai taimaka wajen samun ci gaban tattalin arziki abu ne mai muhimmanci.

Ya ce babban burin gwamnatocin jihohi da na tarayya shi ne samun ci gaban tattalin arziki domin inganta rayuwar al’umma a kowane fanni, tare da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Ya ƙara da cewa Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, na bai wa batun bunƙasa tattalin arzikin jihar muhimmanci a kowane lokaci.

A nasa ɓangaren, Dakta Dayabu Munzali Taura, Uban Doman Ringim, ya ce sama da mutane 7,000 masu zuwa aikin Umara ke tashi daga Kano duk mako.

Ya ce idan aka samu yarjejeniya tsakanin Nijeriya da Saudiyya kan samar da nama ga mahajjata da masu Umara, hakan ka iya taimakawa wajen bunƙasa harkokin kasuwanci da tattalin arziki tsakanin ƙasashen biyu.

Daga cikin waɗanda suka gabatar da jawabai a taron akwai Sheikh Muhammad Sani Sheriff Umar Bichi, shugaban Izala mai shalkwata a Jos, wanda ya ce akwai buƙatar Hukumar Alhazai ta ƙasa ta fifita abubuwan da suke da muhimmanci wajen sauƙaƙa aikin Hajji.

Ya kuma ce ya kamata a guji sanya wa mahajjata wasu ƙarin kuɗaɗe da ba su da muhimmanci.

Ya ce idan, misali, likitoci 100 sun isa kula da lafiyar mahajjata, to a ɗauki likitoci 100 maimakon ƙara adadin zuwa 150 ba tare da wata buƙata ba.

Shi kuwa Alhaji Kazaure, shugaban kula da Adashin Gata na Sauke Farali, ya ce saboda yadda abubuwa suka canza, har yara da aka haifa yau za a iya saka su cikin tsarin tanadin kuɗin aikin Hajji.

Ya ce tanadi ne na dogon lokaci, musamman ganin cewa a halin yanzu hukumomin Saudiyya na buƙatar a yi tanadi tun kafin shekarar aikin Hajjin ta zo domin samun guraben aikin.

A ƙarshe, Dakta Aisha Ahmad, babbar jami’ar shirya taron HUNEXPO2, tare da mataimakiyarta Dakta Fa’iza Haruna Maitala, sun yabawa ɗaukacin masu ruwa da tsaki daga hukumomi daban-daban na ƙasar da suka halarci taron karo na biyu da aka gudanar a Kano.

By ukarofi

Leave a Reply