JAMB ta kori ma’aikaci kan zargin karɓar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu ta Nijeriya (JAMB) ta dakatar da aikin wani daga cikin ma’aikatanta bisa zargin karɓar kuɗi daga wasu ’yan takara, yayin da hukumar ta sake jaddada ƙudurinta na tsaftace tsarin jarabawa da kuma harkar shigar da ɗalibai manyan makarantu.

An bayyana hakan ne a cikin sanarwar hukumar da aka fitar ranar Litinin, inda JAMB ta ce ƙoƙarin da take yi na kawar da damfara da magudi a tsarin ba wai ya tsaya ga masu aikata laifuka daga wajen hukumar kaɗai ba ne, har ma ya shafi ma’aikatan cikin gida da aka samu suna aikata rashin da’a.

Hukumar ta ce matakin da ta ɗauka kan ma’aikacin, wanda ba ta bayyana sunansa ba, ya nuna cewa ƙoƙarinta na kawar da miyagun ma’aikata daga cikin tsarin ya shafi cikin gida da wajen hukumar.

“Inji hukumar, ta dakatar da aikin ɗaya daga cikin ma’aikatanta bisa zargin karɓar kuɗi daga ’yan takara, a matsayin wani ƙarin mataki na nuna ƙudurin da take da shi na kawar da miyagun abubuwa daga cikin tsarin.”

JAMB ta sake gargaɗin dukkan ma’aikatanta da su guji duk wani nau’in rashin ɗa’a, musamman ayyukan da za su iya lalata mutuncin hukumar ko kuma cin moriyar ’yan takara da sauran jama’a, tana mai cewa duk wanda aka samu da irin wannan laifi zai fuskanci hukunci mai tsauri bisa ƙa’idojin da aka shimfiɗa.

Hukumar ta jaddada cewa irin ƙudurin da take amfani da shi wajen yaƙi da masu damfara daga wajen hukumar shi ne za ta yi amfani da shi wajen magance rashin da’a a cikin hukumar.

Ta ce ƙudurin tsaftace tsarin shigar da ɗalibai manyan makarantu da kuma gudanar da jarabawa bai shafi masu damfara daga wajen hukumar kaɗai ba, domin za ta ci gaba da ɗaukar mataki kan duk wani ma’aikaci da aka samu yana aikata rashin da’a ko magudi.

JAMB ta ce korar ma’aikacin na aika saƙo mai ƙarfi ga sauran ma’aikatan hukumar cewa manufarta ta rashin sassauci kan cin hanci da rashawa da rashin da’a ta shafi kowa, ba tare da la’akari da matsayi ko mukamin da yake riƙe da shi ba.

Hukumar ta ƙara da cewa ba za ta kare ko ta yi wa wani ma’aikacinta da ya yi amfani da matsayinsa wajen cin zarafin amincewar da ’yan takara ko jama’a suka ba shi garkuwa ba.

Ta ce bayan da ta ɗauki matakai kan masu damfara daga wajen hukumar da ke neman cin moriyar ’yan takara da jama’a, ba za ta yi wa ma’aikatanta sassauci ba idan suka ketare iyaka ko suka ci amanar amincewar da aka yi musu.

Hukumar ta kuma gargaɗi ma’aikatanta cewa duk wanda aka samu yana aikata abin da zai iya kawo cikas ga ayyukan hukumar zai fuskanci hukunci daidai da ƙa’idojin da aka shimfiɗa.

JAMB ta sake cewa dukkan ma’aikatanta ya kamata su guji duk wani nau’in rashin da’a, musamman ayyukan da za su iya zubar da mutuncin hukumar ko kuma cin moriyar ’yan takara da sauran jama’a, tana mai cewa irin wannan hali zai jawo hukunci mai tsauri bisa ƙa’idojin hukumar.

A ƙarshe, hukumar ta sake tabbatar da aniyarta ta samar da ma’aikata masu gaskiya, rikon amana da ƙwarewa, tana mai jaddada cewa yaƙi da damfara da rashin da’a dole ne ya fara daga cikin hukumar da kanta idan ana son kare mutuncin ayyukanta yadda ya kamata.

By ukarofi

Leave a Reply