Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Cibiyar gwaje-gwajen kimiyya da na jini, Bassam Diagnostic Centre da ke birnin Kano, ƙarƙashin jagorancin Manaja Shamsudden Usaini, ta samu yabo daga wasu manyan likitoci da asibitoci a Kano da kewaye, bisa irin taimakon da take bayarwa ga al’umma da kuma ingancin ayyukan gwajin jini da sauran binciken lafiya da take gudanarwa.
Manajan cibiyar, Shamsudden Usaini, ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai da ya yi a tsakiyar makon da ya gabata.
Ya ce nasarar da Bassam Diagnostic Centre ta samu ta samo asali ne daga samun ƙwararrun ma’aikata da kuma kayan aikin zamani da ake amfani da su wajen gudanar da gwaje-gwajen lafiya.
Ya kuma yaba wa Gwamnatin Jihar Kano, ta hannun Ma’aikatar Lafiya, bisa ɗaukar matakan da suka shafi hana gudanar da ayyukan ƙarin ruwa da ƙarin jini a cibiyoyin lafiya da ba su cika ƙa’idojin da ake buƙata ba.
Shamsudden ya ce bin ƙa’idojin aikin lafiya da amfani da ƙwararrun ma’aikata da kayan aiki masu inganci na daga cikin muhimman abubuwan da ke taimakawa wajen samar da sahihin sakamakon gwaje-gwaje.
A ƙarshe, ya nuna damuwa da takaici kan yadda wasu cibiyoyi ke sauya sakamakon gwajin jini na ainihi bisa son rai ko wasu dalilai na kashin kai.
Ya yi kira da a ƙara zurfafa ilimi da horar da masu aikin wannan fanni, tare da sanya tsoron Allah a cikin aikin, domin, inji shi, aikin kula da lafiyar jama’a amana ce da Allah Ya ɗora a hannun ma’aikatan lafiya.
