Dalilin Shettima na wakilcin Tinubu a taron Majalisar Dinkin Duniya – Idris

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ya umarci Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, da ya wakilce shi a taron babban zauren Majalisar ɗinkin Duniya karo na 81, UNGA, saboda a halin yanzu Shugaban ƙasar yana hutun shekara.

Ministan ya ce Shettima na tafiya ne da cikakken ikon Shugaban ƙasa da kuma wakilcin Tarayyar Nijeriya, yana mai watsi da ra’ayoyin da ke cewa rashin halartar Tinubu da kansa a babban taron na iya rage matsayin Nijeriya a fagen diflomasiyya.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, Mohammed Idris ya ce, “Shugaba Tinubu yana hutun shekara a halin yanzu, kuma shawarar da ya yanke ta tura Mataimakin Shugaban ƙasa ya jagoranci tawagar Nijeriya ba wani sabon abu ba ne, kuma ba ya rage matsayin ƙasar a fagen diflomasiyya.”

Shugaba Tinubu ya umarci Shettima da ya jagoranci tawagar Nijeriya zuwa taron UNGA 81 da ake gudanarwa a birnin New York na ƙasar Amurka, inda ake sa ran Mataimakin Shugaban ƙasar zai gabatar da jawabin Nijeriya na ƙasa tare da halartar tarurrukan manyan ƙasashe da kuma ganawa tsakanin ƙasashe biyu-biyu.

A cewar Mohammed Idris, “Mataimakin Shugaban ƙasa Shettima yana ɗauke da cikakken ikon Shugaban ƙasa da kuma wakilcin Tarayyar Nijeriya.”

Ya ce abubuwan da Shettima zai mayar da hankali a kansu a New York sun haɗa da zaman lafiya da tsaro, bunƙasa tattalin arziki, yaƙi da sauyin yanayi, sake fasalin tsarin kuɗaɗen duniya, ci gaba mai ɗorewa da kuma ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashen duniya.

Ministan ya ce saboda haka Nijeriya za ta samu cikakkiyar wakilci a duk tsawon zaman babban taron.

Bayanin ministan ya zo ne a daidai lokacin da ake ta ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a game da rashin halartar Shugaba Tinubu taron shekara-shekara da ke haɗa shugabannin ƙasashen duniya.

Jakadan Nijeriya na dindindin a Majalisar ɗinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, ya bayyana a watan Yulin 2026 cewa Shugaba Tinubu zai halarci taron UNGA 81 da kansa, inda rahotanni suka ce an shirya wurin zama da zai kasance kusa da Shugaban Amurka, Donald Trump.

Sai dai daga baya fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da cewa Shettima ne zai wakilci Tinubu kuma ya jagoranci tawagar Nijeriya zuwa taron.

An kuma ruwaito cewa Shugaba Tinubu ya bar Abuja a ranar 30 ga Agusta domin fara hutun shekara na tsawon makonni uku a Turai, inda London ta kasance tasharsa ta farko kafin ya wuce zuwa Faransa.

Daga bisani Fadar Shugaban ƙasar ta sanar cewa Tinubu zai dawo Nijeriya bayan hutunsa, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce kan ko zai halarci taron UNGA da kansa.

A ranar Lahadi, 20 ga Satumba, Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima ya tashi daga Abuja zuwa New York domin wakiltar Tinubu a taron Majalisar ɗinkin Duniya na karo na 81.

Babban taron muhawarar UNGA 81 zai gudana daga ranar 22 zuwa 28 ga Satumba, 2026, ƙarƙashin taken “Maido da amincewa, tafiyar da sauyi: Majalisar ɗinkin Duniya da ke samar da sakamako ga kowa.”

Ana sa ran Shettima zai gabatar da jawabin Nijeriya, inda zai bayyana matsayin ƙasar kan manyan batutuwan duniya, tare da halartar tarurrukan manyan ƙasashe da ganawa da shugabannin ƙasashe, ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da abokan hulɗar ci gaba.

A halin yanzu, Shugaba Tinubu ya tsawaita hutun aikinsa na ƙasashen waje da wasu kwanaki, inda Fadar Shugaban ƙasar ta ce ana sa ran zai dawo Nijeriya a ƙarshen mako. Duk da kasancewarsa a hutun, fadar shugaban ƙasar ta ce ya ci gaba da bibiyar al’amuran ƙasar tare da ba da umarni kan wasu muhimman batutuwa.

Mohammed Idris ya kuma yi magana kan sukar rashin halartar Tinubu da wasu ke yi, ciki har da kalaman tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da kuma wata ƙungiyar masu fafutukar diflomasiyya da ke Amurka da aka ce tana aiki a madadinsa.

Ministan ya ce suka da muhawarar siyasa na daga cikin abubuwan da ake samu a tsarin dimokuraɗiyya, amma ya yi gargaɗin kada a gabatar da hasashe ko zarge-zarge a matsayin tabbatattun bayanai.

Ya kuma jaddada muhimmancin dangantakar Nijeriya da Amurka, musamman a fannoni kamar kasuwanci da zuba jari, tsaro, makamashi, cibiyoyin dimokuraɗiyya, zaman lafiyar yankin da hulɗar jama’a tsakanin ƙasashen biyu.

Ya ce dangantakar Nijeriya da Amurka tana gudana ne ta hanyoyin diflomasiyya da hukumomin gwamnati da aka kafa, don haka ya kamata a bambanta ta da kalaman siyasa ko ayyukan ƙungiyoyin masu fafutukar siyasa masu zaman kansu.

Ministan ya yi kira ga ’yan Nijeriya da kafafen yaɗa labarai da su riƙa bambance tsakanin sahihan bayanai, ra’ayoyin siyasa da kuma zarge-zargen da ba su da tabbataccen tushe.

By ukarofi

Leave a Reply