Mutuwar masu haƙar ma’adanai 37: Ba Gwamnatin Neja ke da alhakin biyan diyya ba – Bago

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, ya ce gwamnatin jihar ba za ta biya diyya ga iyalan mutane 37 da suka mutu a hannun Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Nijeriya (NSCDC) ba.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na intanet mai suna Zarar Bunu da ke Minna, wadda aka watsa ranar Lahadi. Ya ce, alhakin biyan diyya bai rataya a wuyan gwamnatin jihar ba, domin mutanen sun mutu ne a hannun wata hukuma ta tsaro da ke ƙarƙashin Gwamnatin Tarayya.

Sai dai Bago ya ce gwamnatin jihar za ta tallafa wa iyalan waɗanda abin ya shafa, tare da yin aiki da hukumomin da abin ya shafa domin ganin an samar musu da taimakon da ya dace.

“Ba mu da hurumin biyan wata diyya, sai dai gwamnatin tarayya. Abin da ya rataya a wuyanmu shi ne tallafa musu,” inji shi.

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa gwamnatin jihar ba za ta biya diyya ba, Bago ya ce abin ya faru ne a Jihar Neja kawai saboda a nan ne aka gudanar da kamen mutanen. “Me ya shafe mu? Abin ya faru ne a jiharmu kawai bisa ƙaddara. Ba mu ne muka tura su (Civil Defence) su kama wani ba. Haka kuma ba mu san da kamen ba,” inji gwamnan.

Bago ya kuma yi zargin cewa NSCDC na da wata alaƙa da wasu daga cikin masu haƙar ma’adinan da aka kama a wuraren haƙar ma’adinai. A cewarsa, Kwamandan NSCDC na jihar ya taɓa sanar da gwamnatin jihar cewa an rufe wuraren haƙar ma’adinan da aka gudanar da kamen.

“An taɓa umartar a rufe wuraren haƙar ma’adinan MI Wushishi, kuma Hukumar Civil Defence, wadda ke da alhakin kula da harkokin haƙar ma’adinai, ta sanar da mu cewa an rufe wuraren. Don haka, daga abin da ya faru yanzu, za ku iya ganin cewa akwai wani abu a tsakaninsu,” inji shi.

By ukarofi

Leave a Reply