‘Yan kwamitin KT1T sun taya Usman Isyaku murnar samun lambar yabo

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mambobin kwamitin shirin Katsina One-Person-One-Tree (KT1T) na Shiyyar Katsina ta tsakiya sun taya Alhaji Usman Isyaku, mai bai wa Gwamna Shawara kan Civil Servicre Reforms, murnar samun lambar yabo ta “Outstanding Special Adviser of the Year 2026.”

An bai wa Alhaji Usman Isyaku lambar yabon ne a bikin cikar Jihar Katsina shekaru 39 da kafuwa, wanda aka gudanar a ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar Katsina Alhaji Farouk Lawal Joɓe.

Mambobin kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Mohammed Al-Amin, tare da Hon. Bishir Tanimu Gambo Dtm, Hon. Lawal Rufa’i Safana da sauran mambobin kwamitin, sun bayyana farin cikinsu, tare da yaba wa Alhaji Usman Isyaku bisa ƙwazo da gudunmawarsa wajen ci gaban Jihar Katsina.

A nasa ɓangaren, Alhaji Usman Isyaku ya gode wa mambobin kwamitin bisa saƙon taya murna, yana mai cewa lambar yabon za ta ƙara masa ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da hidimtawa jihar da al’ummarta.

By ukarofi

Leave a Reply