Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Ɗaruruwan magoya bayan APC sun gudanar da wani gagarumin gangamin goyon baya don Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin sa Kashim Shettima a karo na biyu.
Taron gangamin Grassroots Mobilizers ne suka shirya a yau Asabar domin nasarar Tinubu/Shettima a 2027.
Haka zalika taron ya nuna goyon bayan Sanata Abdulaziz Yari a matsayin darakta janar na majalisar yaƙin neman zaɓen shugaba Tinubu.
Taron gangamin, wanda Ahmad Abdulaziz Yari, memba na kwamitin gudanarwa na majalisar gudanarwa ta ƙungiyar yaran birni watau City Boy da kuma ƙungiyar Grassroots Mobilizers ta shirya don Tinubu da Shettima, ya jawo hankalin dubban magoya bayan APC a faɗin ƙananan hukumomi 14 na jihar.
Taron gangamin, wanda ya ƙare a gidan gwamnati da ke Gusau, magoya bayan sun ta rera waƙoƙin haɗin kai tare da nuna tutoci da fasta na Shugaba Tinubu da Shettima.
Da yake jawabi ga taron, Ahmad Abdulaziz Yari ya ce an kira taron ne don ƙarfafa goyon bayan jama’a ga burin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Dauda Lawal a karo na biyu.
Ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda amincewa da mahaifinsa, Sanata Abdulaziz Yari, a matsayin shugaban yaƙin neman zaɓen na jam’iyyar APC.
“Amincewar mahaifina a matsayin shugaban yaƙin neman zaben ya samo asali ne daga gogewarsa a siyasa da kuma biyayyarsa ga APC da kuma shirin Shugaba Tinubu na sabunta ƙasa watau Renewed Hope Agenda”.
A cewarsa, ƙungiyar ta City Boys da kuma Grassroots Mobilizers sun yanke shawarar yin aiki a matsayin rundunar haɗin gwiwa don tabbatar da nasarar APC a Jihar Zamfara da ƙasa baki ɗaya.
“Wannan gangamin ya shafi aminci, ci gaba da kuma karfafa gwiwa ga matasa da al’ummar jihar Zamfara don samun nasarar APC a zaɓen dake tafe”. Ya ce
Ya yi kira ga matasa a jihar da su kasance cikin lumana, haɗin kai da kuma jajircewa Wajen goyon bayan su ga gwamnatin APC, yana mai tabbatar da cewa za a samu ingattacciyar ribar dimokuraɗiyya.
