EFCC ta kama dakatacciyar shugabar matan tafiyar City Boy Movement kan zargin badaƙala

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, ta ce ta kama Halimat Adenike Tejuosho, wato kodinetar Kudu maso Yamma ta tafiyar City Boy Movement bisa zargin ta da hannu a wani al’amari da ya shafi mallakar wasu kuɗaɗe ta hanyar bayar da bayanan ƙarya.

Rahotanni sun bayyana cewa, kamen na zuwa ne watanni bayan hukumar ta ayyana Tejuosho a matsayin wadda ake nema ruwa-a-jallo kan zargin ta da hannu a wani bincike da ya shafi zargin badaƙalar kuɗaɗe. A watan Afrilu ne EFCC ta ayyana matar mai shekaru 41 a sahun waɗanda take nema.

Kakakin hukumar, Dele Oyewale ne ya sanar da batun kama ta ga jaridar NewsPointNigeria a ranar Asabar, inda ya ce an kama ta ne tun a ranar 8 ga Satumba kuma “tana hannunmu,” inji shi.

A baya ne dai EFCC ta yi kira ga dukkan wanda ya samu wani labari akan inda take da ya sanar da ofisoshinta da ke sassan ƙasar ko kuma dukkan wani ofishin ‘yan sanda mafi kusa. Ta shiga cikin binciken EFCC ne bisa zargin damfara masu alaƙa da ɗaukar da kwangila.

A watan Yunin 2025 ne hukumar ta gudanar da bincike akanta bayan wani ƙorafi da ke cewa ana zargin ta da karɓar kuɗaɗe a hannun mutane da sunan za ta samar musu aikin gwamnati da wasu manyan kwangiloli.

Binciken na EFCC ya fi karkata ne akan zarge-zargen cewa ta yi amfani da takardun ɗaukar aiki na bogi domin ruɗar da su kan cewa tana da hanyar samun aiki ko kwangilar na gwamnati. Bayan ayyana ta a matsayin wadda ake nema ne sai City Boy Movement ta dakatar da ita a muƙamin kodinetar ta shiyyar Kudu maso Yamma, tana mai cewa matakin zai cigaba da aiki har zuwa lokacin da za a kammala bincike.

City Boy Movement tafiyar siyasa ce da ke kira zuwa ga goyon bayan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Ajandarsa ta Sabunta Fata.

By Babaji

Leave a Reply