
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kimanin mutane biyar ne aka halaka da raunata wasu a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki a wani wajen aikin haƙar ma’adinai da ke ƙauyen Marit a Ƙaramar Hukumar Barikin Ladi ta Jihar Sakkwato a ranar Asabar.
Al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1 na rana yayin da jama’a ke gudanar da harkokinsu, wanda ya haddasa firgici kan halin tsaron mazauna da masu aikin haƙar ma’adinai a sassan jihar, wadda take fama da matsalolin hare-hare da kashe-kashe a wasu ƙananan hukumominta.
Wannan na zuwa ne ƙasa da kwana biyar da wasu masu haƙar ma’adinai hudu suka rasu bayan ruftawar wani sashe na wajen da suka aiki a yankin Tangur da ke Ƙaramar Hukumar Ɓokkos.
Kakakin ƙungiyar Matasan Ƙabilar Berom (BYM), Rwang Tengwong ya tabbatar da harin na Marit, inda ya ce mutane biyar ne aka halaka yayin da wasu biyu suka jikkata sakamakon raunuka da sauka samu. Ya bayyana al’amarin a matsayin “abin takaici da ƙunci”, yana mai cewa a wani karon ‘yan ƙauyen sun sake shiga jimamin rashin ‘yan uwansu, yana mai tir da harin.
Tengwong ya kuma kirayi hukumomin tsaro da su gaggauta ƙarfafa matakan tsaro da nufin bayar da kariya ga ƙauyuka da kare hare-hare da ka iya aukuwa a nan gaba.
Wannan al’amari ya sake tayar da ƙura a halin tsaron sassan Filato musamman a ƙauyuka da ke fuskantar hare-hare akai-akai, lamarin da ke tilasta wa mazauna zama a halin ɗar-ɗar yayin da suke gudanar da harkokinsu gonakinsu, haƙar ma’adinai da wasu al’amura na yau da kullum.
