NUEE ta yi barazanar katse lantarkin Nijeriya bisa zargin sojoji da cin zarafin ma’aikatanta

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki ta ƙasa (NUEE) a Jihar Bauchi ta yi barazanar dakatar da ayyukan samar da wutar lantarki a faɗin ƙasar, biyo bayan zargin cin zarafin wasu daga cikin mambobinta da jami’an Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF) suka yi.

Mataimakin Shugaban ƙungiyar NUEE, Rilwanu Shehu, ne ya bayyana hakan a lokacin wata zanga-zangar lumana da ma’aikatan suka gudanar a Bauchi ranar Litinin, 21 ga Satumba, 2026.

Shehu ya ce, zanga-zangar ta samo asali ne daga zargin kutse da kuma cin zarafin wasu daga cikin ma’aikatan ƙungiyar da jami’an Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya suka yi.

Ya bayyana cewa a ranar 18 ga Satumba, wasu jami’an soji sun kutsa cikin ofishin ayyukan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Jos (JEDC) da ke Bauchi, inda suka zargi ma’aikatan wutar lantarkin da katse wutar da ke zuwa wasu wuraren Rundunar Sojin Sama.

A cewarsa, jami’an sun ci zarafin ma’aikatan wutar lantarki tare da tsare mutum 10, inda ya ƙara da cewa waɗanda abin ya shafa suna ci gaba da karɓar magani a gidajensu.

Mataimakin shugaban ƙungiyar ya buƙaci ma’aikatan da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da bin doka, yana mai cewa ƙungiyar tana aiki tare da ’yan sanda da Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) domin ganin an warware lamarin.

Shehu ya ce ma’aikatan suna cikin fargaba kuma ba sa jin cewa suna cikin aminci wajen gudanar da ayyukansu, sai dai ya ce ƙungiyar ta ba hukumomin tsaro, da suka haɗa da ’yan sanda da DSS, damar shiga tsakani domin warware matsalar cikin lumana.

Ya kuma yi barazanar cewa idan ba a ɗauki mataki kan jami’an Rundunar Sojin Sama da ake zargi da cin zarafin ma’aikatan ba, ƙungiyar za ta dakatar da ayyukan masana’antar wutar lantarki a faɗin ƙasar.

Shehu ya ƙara da cewa, ƙungiyar ta bai wa hukumomin da abin ya shafa wa’adin kwanaki uku, daga Litinin 21 zuwa Laraba 25 ga Satumba, domin magance matsalar, ko kuma a fuskanci dakatar da samar da wutar lantarki gaba ɗaya.

Ya zuwa lokacin kammala rahoton, shugabancin Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya a Jihar Bauchi bai ce komai ba kan zargin da ƙungiyar ma’aikatan wutar lantarkin ta yi.

By ukarofi

Leave a Reply