Kotun Sri Lanka ta ɗaure mutane 15 kan harin Easter na 2019

Spread the love

Wata babbar kotu a Sri Lanka ta samu mutane 15 da laifin hannu a harin kunar bakin wake da aka kai a ranar Easter ta 2019, wanda ya kashe sama da mutane 260 tare da jikkata ɗaruruwan wasu.

Harin na 21 ga Afrilu 2019 ya shafi majami’u uku da manyan otal-otal uku a sassan ƙasar, lamarin da ya zama ɗaya daga cikin hare-haren da suka fi muni a tarihin Sri Lanka tun bayan kawo ƙarshen yakin basasa na ƙasar. 

Rahotanni sun ce 15 ɗin an same su da hannu wajen shirya ko taimakawa waɗanda suka kai harin, yayin da wasu tara da ake tuhuma a shari’ar aka wanke su. Mutanen da suka kai harin da kansu duk sun mutu a lokacin da bama-baman suka tashi. 

An gabatar da dubban tuhume-tuhume kan waɗanda ake zargi da hannu a lamarin, ciki har da kisan kai, shirya ta’addanci da kuma mallakar makamai da abubuwan fashewa.

Hukumomin Sri Lanka sun sha fuskantar suka kan yadda aka yi watsi da bayanan sirri da suka yi gargadin yiwuwar kai harin kafin aukuwarsa. A watan Yuli ma, an yanke wa wasu tsoffin jami’an tsaro hukuncin kisa kan gazawar da aka ce sun yi wajen ɗaukar mataki bayan samun bayanan sirrin. 

By ukarofi

Leave a Reply