An sake ɗage dawowar Tinubu Nijeriya zuwa Talata

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya ɗage dawowarsa zuwa Nijeriya bayan wani sauyi da aka samu acikin jaddawalin tsare-tsaren tafiyarsa.

Da fari dai an yi tsammanin shugaban ya dawo Nijeriya a yau Lahadi, amma a yanzu a samu sauyi inda ake sa ran ya dawo a Talata. Saidai ba a bayyana dalilinsa ba na ɗaukar wannan mataki har zuwa safiyar Lahadi.

Majiyoyi daga fadar Shugaban Ƙasa sun shaida wa manema labarai cewa shugaban da zai dawo Nijeriya ne a yau Lahadi, kamar yadda aka tsara bayan shafe makonni yana hutu a Nahiyar Turai.

A yanzu dai bisa sababbin bayanan da aka samu, Tinubu zai dawo Nijeriya a ranar Talata bayan shafe sama da makonni huɗu a Nahiyar Turai.

Tun a ranar 30 ga Agusta ne dai Shugaban ya bar Nijeriya zuwa Landon kana daga bisani ya garzaya Paris na ƙasar Faransa a matsayin ɓangare na tafiya hutunsa na shekara.

By Babaji

Leave a Reply