Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Bayanai daga karamar hukumar Jega da ke jihar Kebbi sun nuna yadda waɗansu fusatattun matasa suka shiga garin Jega suna farfasa motoci da yaga allunan Tinubu da gwamnan jihar Malam Nasir Idris bayan kammala wani wasan ƙwallon kafa.
Wani matashi ya bayyanawa wakilin Jaridar Blueprint Manhaja da cewa bayan an kammala wasan ƙwallon ƙafa ne na haɗin kan matasa sai ɗaya daga cikin masu jawabi ya bijiro da maganar neman goyon bayan shugaban ƙasa Tinubu da gwamnan jihar Kebbi Malam Nasir Idris wanda wannan maganar ba ta yi wa kowa daɗi ba wanda a maimakon ya jajentawa al’ummar wannan yankin da ‘yan bindiga suka tarwatsa garuruwan su amma sai ya ɗauko maganar siyasar Tinubu da Kaura.
Bayan an watse matasa suka shiga garin Jega suna yaga allunan Tinubu da kuma farfasa gilashin motoci. Ya ƙara da cewa yanzu haka garuruwa da da suka haɗa Katanga,Alelu, Jan Dutsi, Kimba da sauran ƙauyukan da da ke gabas da Jega kusan duk an tarwatsa su suna nan cikin garin Jega a matsayin yan gudun hijira amma har kawo yanzu babu wani agaji ko saƙon jaje daga gwamnati sannan wani ya zo yana tallata Tinubu saboda rashin Imani.
Alhaji Sanusi Jayewa 11 Motors yana daga cikin waɗanda abin ya rutsa da su inda shi ma matasan sun kai farmaki a kamfanin sa suka farfasa gilashin motocin da ke kamfanin ya bayyana cewa ana zargin wasu ’yan jam’iyyar ADC da hannu wajen aika wasu matasa wurin masu kallon ƙwallo domin tayar da tarzoma da kuma ƙoƙarin haɗa shi da faɗa da Gwamnan Kebbi, Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu.
“Muna zargin ’yan jam’iyyar ADC ne suka tura wasu matasa wajen masu kallon ƙwallo, domin su tayar da tarzoma tare da ƙoƙarin haɗa ni faɗa da Mai Girma Gwamna, Dr. Nasir Idris Ƙauran Gwandu,” inji shi”
Haka-zalika Jayewa 11 ya ce yana ganin akwai matsala wajen yadda waɗansu daga cikin mutanen da ke zagaye da gwamnan ke karɓar koke-koken jama’a, yana mai cewa rashin ɗaukar waya ko isar da matsaloli ga gwamna na iya sa ƙananan matsaloli su girma.
