
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Fadar Shugaban Ƙasa ta yi watsi da yadda ake nuna damuwa kan inda Shugaba Bola Tinubu yake da rashin halartarsa a taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 81 a New York, tana mai cewa Shugaban yana nan “cikin ƙoshin lafiya” kuma yana bakin aiki.
Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ne ya bayyana haka a wani saƙo da ya wallafa a Facebook a yammacin ranar Lahadi, inda yake bayar da amsa akan tambayoyin da tsohon gwamnan Jihar Anambara kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi da wasu suke yi kan daɗewar shugaban a waje.
Onanuga ya ce, Tinubu yana da ‘yancin hutunsa na shekara kuma babu buƙatar sai ya kasance a Abuja sannan zai gudanar da ayyukansa na dokar ƙasa, musamman a wannan zamani na ci-gaba, inda yake kasancewa tare da jami’an gwamnati a kodayaushe. Ya ce, shugaban ƙasar ya cigaba da aiki yayin da yake hutu a Nahiyar Turai, inda yake ganawa da masu zuba jari a Faransa.
Ya bayyana cewa, a ranar 24 ga Satumba Tinubu ya shaidi ƙulla yarjejeniya tsakanin Gwamnatin Jihar Ogun da kamfanin waje DP World domin ci-gaban tashar ruwa ta Gateway Deep Seaport a gaɓar ruwan Jihar da kuma sashen tattali na Ogun Blue Marine Special Economic Zone. Ana tsammanin ayyukan za su lanƙwame jimillar Dala biliyan 7 a tashin farko, ciki har da tashar deep-sea da sashen tattali na musamman mai faɗin hecta 10,000 da nufin rage matsi ga tashoshin jiragen ruwan Jihar Legas.
A cewarsa, fadar shugaban ƙasa ta sanar da cewa Tinubu ya bar Nijeriya ne a ranar 30 ga Agusta domin fara hutunsa na shekara, inda ya fara yasar da zango a Landon, sannan ya je Paris a Faransa ya gana da Shugaba Emmanuel Macron na ƙasar da kuma Attajiri Vincent Bolloré.
Ya ƙara da cewa, Tinubu ya cigaba da bada umarnin gudanar da harkokin mulkin Nijeriya, ciki har da umartar a gudanar da bincike mai zaman kansa akan al’amarin mutuwar masu haƙar ma’adinai guda 37 a ofishin Hukumar Sibil Difens na jihar Neja. Sannan, ya wakilta Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya jagoranci tawagar Nijeriya a taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA na 81) da kuma gabatar da jawabin ƙasar, yana mai cewa kasancewar ba ya Nijeriya ba sabon abu ba ne a dokance.
Kazalika, Onanuga ya ce akwai shugabannin ƙasashe da dama da ba su samu halartar taron ba, inda ya bayar da misali da Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu da na Misra, Abdel Fattah el-Sisi, waɗanda suka wakilta wasu jami’an gwamnatocinsu a taron.
