
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya dawo gida Nijeriya bayan tsawaita zamansa a nahiyar Turai.
Manhaja ta ruwaito cewa, Shugaban ya isa birnin Legas ne daga Paris ta jirgin ƙasa a ƙarƙashin ikon Sojojin Sama na Nijeriya, wanda ya sauka a filin jiragen sama na Murtala Muhammed da misalin ƙarfe 6:32 na yammacin ranar Talata.
An ga yadda aka hana ‘yan jarida ɗaukar hoto ko bidiyon isowar Shugaban Nijeriyar, yayin da aka taƙaice adadin ‘yan jarida a lokacin da jirgin yake ƙoƙarin ƙarasawa zuwa wajen ajiyarsa.
A ranar 30 ga Agusta ne Shugaba Tinubu ya bar Nijeriya zuwa Landon kana daga bisani ya garzaya Paris a ƙasar Faransa, inda ya gana da Shugaba Emmanuel Macron, ciki har da cin abincin dare tare.
Ana tsammanin shugaban ya shiga harkokin bikin cikar Nijeriya shekeru 66 da samun ‘yancin kai a ‘yan kwanaki kaɗan masu zuwa.
