Gombe: Mailantarki ya ƙi amince wa sakamako bayan Pantami ya sake lashe zaɓen fidda gwanin PDP

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya sake zama ɗan takarar gwamnan jihar Gombe a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP a zaɓen 2027 bayan da ya lashe sabon zaɓen fidda gwanin da jam’iyyar ta gudanar a gundumomi 114 na faɗin ƙananan hukumomin jihar.

An gudanar da zaɓen fidda gwanin ne a ranar Talata a faɗin ƙananan hukumomi 11 na jihar, bayan hukuncin Babbar Kotun Gombe na ranar Alhamis da ya soke fitar da Pantami a matsayin ɗan takara a karon farko da PDP ta yi da kuma umartar ta sake gudanar da sabon zaɓe. Kotun ta ce hanyoyin da aka bi wajen tsayar da Pantami a matsayin ɗan takarar jam’iyyar da fari, sun saɓa wa hukunce-hukuncen zaɓe, don haka ta ɗauki matakin sokewa da neman a sake gudanar da wani zaɓe domin tabbatar da adalci.

Da yake sanar da sakamakon zaɓen na Talata, Shugaban kwamitin zaɓen fidda gwanin PDP, Hon Johnbull Tiemlong Shekarau, ya ce jimillar mambobi 2,555 ne suka shiga zaɓen. Ya bayyana cewa, Pantami ya samu ƙuri’a 2,054, lamarin da ya ba shi nasara akan tsohon ɗan majalisar wakilai, Khamisu Ahmed Mailantarki da Hon. Usman Aliyu Garry. A cewarsa, Mailantarki ya samu ƙuri’a 389 a matsayi na biyu, yayin da Garry ya samu ƙuri’u 112, matsayi na uku.

Saidai wannan sakamakon na neman tayar da ƙura bayan da Mailantarki ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen duk da cewa shi ne wanda aka sanar ya zo na biyu bayan kammalawa. Da yake ganawa da manema labarai jim-kaɗan bayan sanar da sakamakon, Mailantarki ya ce bisa la’akari da hukuncin Kotun Ƙoli, bai dace Pantami ya shiga sahun ‘yan takara ba a zaɓen fidda gwanin.

Ya bayyana cewa Pantami ɗan jam’iyyar APC ne a lokacin da kwamitin tantancewar PDP ya tantance ‘yan takarar da za su shiga zaɓen fidda gwani da aka shirya a ranar 26 ga Mayu, 2026, yana mai cewa shi da Garry ne kaɗai suka cancanci shiga sabon zaɓen. A cewarsa, zai ƙalubalanci sakamakon a kotu bisa la’akari da ‘yancin da doka ta ba shi. A baya dai Mailantarki ya ƙalubalanci ayyana Pantami a matsayin ɗan takara, inda daga bisani babbar kotun Gomben ta umarci a sake sabon zaɓe.

A jawabinsa na karɓa, Farfesa Isa Ali Pantami ya yaba wa mambobin jam’iyyar kan gudanar da zaɓen cikin lumana tare da kira ga Mailantarki da Garry da su haɗa hannu da shi wajen kai jam’iyyar ga nasara a zaɓen 2027, yana mai alƙawarin ɗora jihar Gombe akan ingantacciyar turbar jagoranci muddin suka samu nasara.

By Babaji

Leave a Reply