
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya ce ya ji daɗin hutunsa na makonni huɗu da ya yi a nahiyar Turai kuma ya dawo Nijeriya cikin “ƙoshin lafiya da shiryawa tsaf domin cigaba da gudanar da harkokin mulki”.
Tinubu ya yi wannan jawabi ne a ranar Talata yayin da ya dawo Legas daga Paris ta ƙasar Faransa, ind ya shafe ɓangare na ƙarshe na hutun nasa a Turai.
Shugaban ya kuma bayar da amsa game tambayoyi akan damuwa da wasu ‘yan Nijeriya suka nuna ciki har da masu masa fatan alheri musamman kan halin lafiyarsa. “Na shirya tsaf, a shirye nake a cigaba. Babu wani abin da yake faruwa”, inji shi.
Ya ƙara da cewa, za a cigaba da yaɗa jita-jita a fage siyasa, amma kuma a haƙiƙanin gaskiya yana nan cikin ƙoshin lafiya.
A ranar 30 ga Agusta ne dai Tinubu ya bar Abuja zuwa Turai domin fara hutunsa na shekara, inda ya yada zango a Landon. Daga bisani fadar shugaban ƙasa ta sanar da cewa an ƙara wa’adin hutun nasa da ‘yan kwanaki.
