El-Rufai na girbar abin da ya shuka a Kaduna ne – Shehu Sani

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya ce tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, na girbar sakamakon abubuwan da ya aikata a lokacin da yake mulkin jihar. Ya ce halin da tsohon gwamnan ke ciki a yanzu ya kamata ya zama darasi ga sauran shugabanni.

Shehu Sani da El-Rufai sun daɗe suna takun saƙa a siyasar Kaduna, musamman a lokacin da El-Rufai ke matsayin gwamnan jihar daga shekarar 2015 zuwa 2023.

Rikicin da ke tsakaninsu ya tsananta ne a lokacin da Shehu Sani ke matsayin Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, inda ya yi adawa da wasu buƙatun gwamnatin El-Rufai na karɓar bashi.

A lokacin, Majalisar Dattawa ta yi watsi da buƙatar gwamnatin Kaduna na karɓar bashin dala miliyan 350 daga Bankin Duniya, bayan Shehu Sani, wanda ke jagorantar kwamitin majalisar kan basuka, ya ƙalubalanci buƙatar.

Da yake magana a wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Juma’a, Shehu Sani ya ce El-Rufai na girbar abin da ya shuka a lokacin mulkinsa.

Ya zargi gwamnatin El-Rufai da amfani da ƙarfin gwamnati wajen murƙushe abokan hamayya da kuma tsare wasu daga cikinsu, yana mai cewa irin waɗannan abubuwa na daga cikin abubuwan da ya kamata shugabanni su yi la’akari da su yayin da suke riƙe da madafun iko.

Shehu Sani ya kuma zargi gwamnatin El-Rufai da rashin ɗaukar matakan da suka dace wajen magance matsalar tsaro, musamman a Kudancin Kaduna.

Ya kuma yi zargin cewa an nuna wariya a lokacin mulkin El-Rufai, yana mai cewa halin da tsohon gwamnan ke fuskanta a yanzu ya kamata ya zama darasi ga sauran shugabanni cewa mulki na wucin gadi ne, kuma ya kamata masu riƙe da madafun iko su yi amfani da damar da aka ba su wajen gudanar da mulki bisa doka da adalci.

By ukarofi

Leave a Reply