Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ruwan sama mai ƙarfi ya haddasa ambaliyar ruwa a wasu sassa na birnin Port Harcourt, babban birnin Jihar Rivers, inda ruwa ya mamaye gidaje da tituna tare da nutsar da motoci, lamarin da ya bar wasu mazauna yankunan cikin mawuyacin hali tare da kawo cikas ga harkokin yau da kullum.
Rahotanni sun bayyana cewa ambaliyar ta biyo bayan ruwan sama mai ƙarfi da aka shafe kwanaki ana samu a birnin, inda wasu mazauna yankunan da abin ya shafa suka makale tare da kasa gudanar da harkokinsu yadda ya kamata.
Hotunan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna yadda ruwan ambaliyar ya kai sama da kugu a wasu wurare, yayin da wasu mazauna ke ƙoƙarin ceto kayayyakinsu daga ruwan da ke ci gaba da hauhawa.
Yankunan da aka ruwaito ambaliyar ta shafa sun haɗa da Chiomana Street da ke Rukpokwu, wasu sassan hanyar Aba Eɗpressway, Peter Odili Road, Ozuoba da sauran wurare. Wasu rahotanni kuma sun ambaci New GRA, Eliozu, Eneka, Elimgbu, SARS Road, Rumuokwuta, Obiwali Road, Aba Road da NTA Road cikin wuraren da suka fuskanci ambaliyar.
An ga motoci da dama sun nutse cikin ruwa, yayin da wasu mazauna da suka makale a gidajensu ke ƙoƙarin kwashe ruwan da ya shiga gidajensu. An kuma bayar da rahoton lalacewar wasu sandunan wutar lantarki sakamakon ambaliyar.
Ambaliyar ta kuma kawo cikas ga harkokin ilimi da sauran ayyukan zamantakewa a yankunan da abin ya shafa, inda wasu ɗalibai suka kasa zuwa makarantu saboda hanyoyin da ruwa ya mamaye. Haka kuma, wasu baƙin da suka halarci wani biki na aure a ƙarshen mako sun makale bayan ambaliyar ta mamaye wurin da aka shirya gudanar da liyafar.
Sharar gida da najasa da ruwa ya kwashe suka taru a saman ambaliyar, lamarin da ya ƙara jawo fargabar yiwuwar barkewar cututtuka da ke da alaƙa da gurɓataccen ruwa a tsakanin mazauna yankunan.
Ambaliyar, wadda ruwan sama mai tsanani ya haddasa, an danganta ta da wasu abubuwa da suka haɗa da matsalolin tsara birane, toshe hanyoyin ruwa na halitta da kuma zubar da shara ba bisa ƙa’ida ba. Sai dai wasu rahotanni sun nuna cewa ruwan sama mai ɗorewa da ƙarancin damar magudanan ruwa na ɗaukar yawan ruwan sun taimaka wajen tsananta matsalar.
Haka kuma, ci gaban gine-gine a wasu wuraren da a baya suke matsayin hanyoyin da ruwan sama ke bi zuwa wasu wurare ya zama wani abu da ake dangantawa da ƙara tsananta ambaliyar, musamman a lokacin da aka samu ruwan sama mai yawa.
Wasu mazauna yankunan da ambaliyar ta shafa sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta kawo musu ɗauki, suna cewa ba su da wani wuri da za su koma yayin da ruwa ke ci gaba da mamaye gidajensu da muhallansu.
Rahotanni sun ce matsalar ta kuma shafi wasu sassan Obio/Akpor da ke makwabtaka da Port Harcourt, inda gidaje, tituna, gonaki da wuraren kasuwanci suka fuskanci ambaliyar ruwa.
A lokacin da aka gabatar da rahoton, gwamnatin Jihar Rivers ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan ambaliyar ba.
Sai dai ambaliyar ta sake janyo kira ga hukumomi da su inganta tsarin magudanan ruwa, kare hanyoyin ruwa na halitta tare da ɗaukar matakan dogon lokaci domin rage barazanar ambaliyar da ke yawan faruwa a birnin Fatakwal a lokacin damina.
