’Yan sanda sun kama matar aure bisa zargin kashe kishiyarta da turmi a Bauchi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama wata matar aure mai shekaru 33, Hauwa’u Haruna, bisa zargin kashe kishiyarta, Jamila Adamu, mai shekaru 43, da turmi a Tafawa Balewa Housing Estate da ke cikin birnin Bauchi.

Lamarin ya faru ne ranar 27 ga Satumba, 2026, inda daga bisani rundunar ’yan sandan jihar ta kama wadda ake zargin bayan samun bayanai kan rikicin cikin gida da ya faru tsakanin matan aure biyu da ke zaune a gida ɗaya na mijinsu.

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, SP Nafiu Habib, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Bauchi.

Habib ya ce da misalin ƙarfe 4:05 na yamma ranar 27 ga Satumba ne Sashen ’Yan Sandan C-Division da ke Bauchi ya samu sahihin bayani game da wani rikicin cikin gida da ya shafi matan aure biyu da ke zaune a gida ɗaya.

Ya bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa matar aure ta biyu, Hauwa’u Haruna, mai shekaru 33, wadda ake zargin tana cikin yanayin ruɗani, ta ɗauki turmi sannan ta bugi matar aure ta farko, Jamila Adamu, mai shekaru 43, a goshinta, lamarin da ya sa ta faɗi cikin rashin sani.

Mai magana da yawun rundunar ya ce jami’an bincike na C-Division sun gaggauta zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka rubuta bayanan abin da suka gani tare da kwashe wadda abin ya shafa zuwa Asibitin Kwararru na Bauchi domin samun kulawar lafiya.

Sai dai ya ce likita ya tabbatar da cewa Jamila Adamu ta rasu, bayan haka aka ajiye gawarta a dakin ajiyar gawa na asibitin domin gudanar da binciken gawar.

A halin yanzu, rundunar ’yan sanda ta kama wadda ake zargin, yayin da aka kwato turmin da ake zargin an yi amfani da shi wajen aikata laifin a matsayin hujja.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya bayar da umarnin tura shari’ar zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jiha (SCID) domin gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.

Kwamishinan ya jajanta wa iyalan marigayiyar tare da yin kira ga jama’a da su guji tashin hankalin cikin gida. Ya kuma shawarci iyalai da su nemi taimakon likita da na ƙwararrun masu kula da lafiyar kwakwalwa cikin lokaci idan suka lura wani daga cikin ’yan uwansu na fuskantar matsalolin lafiyar kwakwalwa.

By ukarofi

Leave a Reply