Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali kan siyasa yanzu, domin lokacin siyasa ya yi.
Gwamnan ya bayyana hakan yau Asabar, a wajen taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar da ke Gusau.
Gwamna Lawal ya ce tsawon shekaru uku da suka gabata, gwamnatinsa ta mayar da hankali ne wajen gudanar da ayyukan gwamnati don al’ummar jihar, inda ya lura cewa yanzu lokaci ya yi na fuskantar siyasa.
“Tsawon shekaru uku mun mayar da hankali ne kan gudanar da gwamnati. Yanzu kuma lokaci ya yi da za mu koma kan siyasa, saboda lokacinta ya yi,” in ji Gwamnan.
Da yake magance ƙorafe-ƙorafe wasu ‘yan jam’iyya da ke cewa ba su amfana da komai ba daga gwamnati, Gwamna Lawal ya ƙaryata wannan ikirari, inda ya ƙalubalanci duk wani kwamishina da ke ganin bai amfana ba ya yi murabus.
“Akwai wasu da ke ƙorafin cewa ba su samu komai ba. Wannan ba gaskiya ba ne. Ko a cikin kwamishinoni, duk wanda yake ganin ba ya samun komai, ya aje,” in ji shi.
Ya amince cewa kuskuren da gwamnati ta yi shi ne rashin bayyana sunayen waɗanda aka ba wa kwangiloli, inda ya yi alkawarin cewa za a bayyana sunayen.
Gwamnan ya lissafa wasu muhimman jiga-jigai na jam’iyyar da suka haɗa da Zannah, Mai Palace, Hon. Aminu Jaji da Hon. Bello Hassan, yana mai cewa sun gudanar da shirye-shiryen tallafawa al’umma da matasa a jihar.
Sai dai ya yi kira ga ‘yan jam’iyya da su yi haƙuri, yana mai cewa babu wani mutum ɗaya da zai iya biya wa kowa buƙata.
“Daga yau, don Allah, mu daina siyasar gidan wane da gidan wane. Mu zo mu dunƙule wuri guda. Ba maganar ɗan gidan Dauda, Matawalle ko Shehi ba; mu zo mu zauna wuri guda, saboda Allah ne ya haɗa mu cikin ni’imarsa,” in ji Lawal ya yi kira.
Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa gwamnatinsa ta aiwatar da ayyuka da suka kai aƙalla naira biliyan 20 a kowace daga cikin ƙananan hukumomi 14 na jihar.
Ya kuma ce matasa sama da dubu 3000 aka horar da su tare da ba su kuɗin sufuri, yana mai cewa ana tallafawa waɗanda suka kammala karatu domin su dogara da kansu, inda ake kiyaye jerin sunayen waɗanda ke amfana a kowane wata.
Game da yaƙin neman zaɓe mai zuwa, Gwamnan ya bayyana cewa zai gana a Abuja da tsoffin Gwamnonin Jihar, Yarima, Mamuda Shinkafi, Abdulaziz Yari da Bello Matawalle domin haɗawa da kammala jerin sunayen waɗanda za su jagoranci yaƙin neman zaɓen APC a Jihar Zamfara.
“Don Allah, ko da ba ka ga sunanka ba, kada ka ɗauka cewa ba ka da muhimmanci. Wallahi, kowa yana da muhimmanci, sai dai ba za a iya saka kowa ba,” in ji shi.
Gwamna Lawal ya tabbatar da cewa ya ji kuma ya lura da dukkan ƙorafe-ƙorafen da aka gabatar a wajen taron, inda ya yi alƙawarin fito da tsare-tsare domin tabbatar da kowa ya amfana.
