Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya yi kira na musamman ga membobin masu yi wa ƙasa hidima ta NYSC 2,617 da aka tura jihar cewa kada su raina gudummawar da za su iya bayarwa wajen cigaban jihar.
Gwamna Sule ya yi wannan kiran ne a jiya Juma’a yayin bikin rantsar da aji na 2026 Batch ‘C’ Stream I a sansanin Magaji Dan Yamusa na din-din-din da ke Keffi.
Gwamnan wanda kwamishinan matasa da wasanni Mista Jubril Ibrahim ya wakilta ya buƙaci masu yi wa ƙasar hidima da kada su ɗauki tura su zuwa al’ummomi bayan atisayen makonni uku a matsayin sharadi kawai na kammala shekarar bautar ƙasa illa a matsayin dama ta bayar da gagarumar gudummawa.
“Kada ku raina kimar ƙananan abubuwan da za ku iya yi. Malami da ya zaburar da yaro, ma’aikacin lafiya da ya yi wa al’ummar karkara hidima da jajircewa, mai sa kai da ya tattara matasa don ci gaba, ko dan bautar ƙasa da ya gabatar da wani sabon ƙirƙire-ƙirƙire mai amfani zai iya kawo sauyi mai ɗorewa,” in ji shi.
Sule ya taya masu yi wa ƙasar hidima murna bisa kammala karatunsu cikin nasara wanda ya ba su damar yin bautar kasar, yana mai cewa an kafa shirin NYSC ne domin ƙarfafa haɗin kan ƙasa da ci gaban al’umma ta hanyar ladabtarwa da kishin ƙasa a matsayin wani muhimmin ɓangare na ci gaban tattalin arzikin ƙasa.
“A yau ne aka fara wani muhimmin babi a rayuwarku. Shirin yi wa ƙasa hidima na NYSC ya kasance ɗaya daga cikin kayan aikin da suka fi ɗorewa wajen inganta haɗin kan kasa, ƙarfafa kishin ƙasa da kuma ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin al’ummominmu daban-daban,” in ji shi.
Yace shirin ya yi tasiri mai kyau a rayuwar miliyoyin mutane a Jihar Nasarawa, musamman a karkara inda ‘yan bautar ƙasa suka ba da gagarumar gudummawa wajen ilimantar da yaranmu da kuma gudanar da ayyukan raya al’umma.
Gwamnan ya kuma nanata muhimmancin matasa a matsayin jami’an cigaban tattalin arziki kowacce ƙasa inda ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta cigaba da haɗa kai da tallafawa ƙoƙarin shirin NYSC wajen cimma manyan manufofinsa.
Ya yi kira ga ‘yan bautar ƙasar da su kula da darussan da horon soja da za su samu yayin da suke sansani, yana mai cewa waɗannan ƙoƙarin za su ci gaba da karfafa karfinsu na jiki da na kwakwalwa wanda zai shirya su don manyan ayyuka a gaba.
“Ina umartarku da ku kasance masu bin rantsuwar da kuka yi a dan lokacin da ya wuce. Saboda haka, ina sa ran za ku nuna ruhin biyayya, ladabi, aiki tukuru da kuma kishin kasa wajen yi wa ƙasarmu hidima.
“Ina so in tabbatar wa hukumomin NYSC da ‘yan bautar ƙasar cewa gwamnatin Jihar Nasarawa za ta ci gaba da haɗa kai da NYSC da hukumomin tsaro masu dacewa don tabbatar da walwala da tsaron ‘yan bautar ƙasa da ke yi wa jihar hidima,” in ji shi.
A nata jawabin kodinetan shirin a jihar Hajiya Salamatu Muhammad, ta gode wa gwamnan bisa halartarsa da kuma goyon bayan da gwamnatinsa ke bai wa shirin NYSC a jihar.
Ta bayyana cewa kwas ɗin horon ba wai shiri ne na yau da kullum kawai ba a’a kwarewa ce da aka tsara domin gabatar da ‘yan bautar ƙasa ga ɗabi’u, manufofi da hangen nesa na NYSC.
Salamatu Muhammad tace jimillar ‘yan bautar kasa 2,617 da suka haɗa da maza 1,215 da mata 1,402 ne suka yi rajista cikin nasara don horon, tana mai cewa tun isowarsu ‘yan bautar ƙasar sun nuna ƙwazo, juriya, daidaitawa da kudurin cin gajiyar ƙwarewar.
Ta tabbatar wa ‘yan bautar ƙasar cewa hukumar NYSC da jami’an sansanin sun himmatu wajen sanya ƙwarewarsu ta zama mai amfani amma shigarsu sosai zai taimaka wajen cimma wannan manufa.
