Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Tsohon Shugaban soja na Jihar Zamfara, Kanal Jibrin Bala Yakubu (mai ritaya), ya yaba wa gwamnatin Gwamna Dauda Lawal saboda sake fasalin jihar ta hanyar bunƙasa tattalin arzikin ɗan Adam da kuma sauyi mai ingancin a Jihar.
Kanal Yakubu ya yi wannan sanarwar ne a ranar Juma’a a Gusau yayin da yake buɗe sakatariyar J.B Yakubu da aka gyara a matsayin wani ɓangare na ayyukan bikin cika shekaru 30 da kafa Jihar Zamfara.
Da yake jawabi a wurin bikin, ya ce ya yi matuƙar farin ciki da ci gaban da gwamnatin yanzu ta samu.
“Abin da na gani shi ne gagarumin sauyi a Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal,” in ji shi.
A cewarsa, shirin ceton Jihar ta Zamfara da Gwamna Lawal ya ayyana ya shafi ci gaban zamantakewa da tattalin arziki na jihar zuwa manyan matakai, wanda hakan ya dawo da martabar Jihar da ƙwarin gwiwa ga shugabanci.
Kanal Yakubu, wanda shi ne gwamnan soja na farko a jihar a lokacin da aka kafa ta a shekarar 1996, ya amince da Gwamna Lawal a karo na biyu a kan mulki, yana mai kira ga mutanen Zamfara da su goyi bayan gwamnatinsa don ci gaba da bunƙasa jihar.
A farkon jawabinsa, Gwamna Dauda Lawal ya yaba wa tsohon Gwamnan soji saboda goyon bayan da yake bai wa jama’a da gwamnatin jihar Zamfara ba tare da wata matsala ba.
Gwamnan ya bayyana Kanal Yakubu a matsayin uba kuma dattijo wanda gudummawar sa ta kafa harsashin jihar.
Gwamna Lawal ya ce gwamnatinsa ta ƙuduri aniyar bunƙasa jihar ta hanyar samar da kayayyakin more rayuwa wanda ke da tasiri kai tsaye ga rayuwar jama’a.
Ya lura cewa gyaran da aka yi da sanya wa sakatariyar jihar sunan Kanal JB Yakubu yana nuna rawar da ya taka a baya da kuma sadaukarwar da ya yi wajen gina Zamfara tun daga farko.
