NLC ta tabbatar da tsarin fansho na da alfanu ga ma’aikatan Katsina – Mai’adua

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa reshen jihar Katsina NLC ta sake nanata cewa tsarin fansho da gwammatin jihar ta ɓullo da shi mafita ce mai ɗorewa bayan aje aiki ga ma’aikata.

Muƙaddashin shugaban ƙungiyar, Kwamarad Nasiru Wada, ya bayyana haka a yayin zantawa da manema labarai dan gane da saƙon ƙungiyar na cikar Nijeriya shekaru 66 da samun yancin kai.

Comrade Nasiru Wada yayi nuni da cewa babu yanda za’ayi ƙungiyar ta bari ayi amfani da wani tsari wanda zai cutar da ma’aikata kasancewar su sune jigon nasarar cigaban Nigeria a tsawon shekaru 66.

“A koda yaushe ƙungiyar ƙwadago tsaye take don tabbatar da bunƙasa jin daɗi da walwalar ma’aikata don duk kan wani abu da za’a ɓullo da shi sai mun tabbatar da alfanun shi ga ma’aikata,”Kwamred Wada Mai’adua ya ce.

Ya bayyana cewa shi tsarin fansho zai kasance tsari mai aminci wanda zai taimaki ma’aikata wajen samun hakkokinsu da zarar sun aje aiki.

Mai’adua ya ƙara da cewa, daga cikin matakan da aka cimmawa tsakanin gwamnati da ƙungiyar shine warware duk basukan da ke tsakanin gwamnati da yan fansho wanda kuma gwamnatin ta fara haka ta hanyar sakin miliyan dubu 45 don fara warware basukan haƙƙoƙin ma’aikatan da suka aje aiki.

Muƙaddashin shugaban ƙungiyar ya kuma yi nuni da cewa reshen ƙungiyar tare da shugabancin ƙungiyar na ƙasa sun fara shirye-shiryen tattaunawa kan sabon tsarin albashi.

Kwamarad Nasiru Wada ya kira ga ma’aikata da su cigaba da jajircewa a kan gaskiya da riƙon amana don sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.

By ukarofi

Leave a Reply