Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Majalissar dokoki ta jihar Katsina, ta yi karatu na 2, akan dokar dake buƙatar yiwa kundun tsarin mulkin Nijeriya garambawul, domin ƙirƙirar ‘yan sandan jihohi.
Majalissar ta karɓi buƙatar yin dokar, domin yiwa kundun tsarin mulkin garambawul daga majalissar ƙasa (National Assembly) bayan da majalissar ta rattaɓa hannun a kan dokar, domin ƙirƙirar ‘yan-sandan. Yanzu kuma majalissar ta tura dokar zuwa majalissun dokokin Nijeriya, domin neman amincewar su.
Bayan amincewa da majalissar ƙasa tayi da dokar, dole ne sai an tura kundun dokar zuwa majalissun jihohi 34 dake faɗin Nijeria domin amincewar su, dokar ba za ta tabbata ba, har sai an samu goyan baya daga biyu bisa ukkun, majalissun dokokin.
Bayan yiwa dokar karatu na biyu, majalissar ta ƙirƙiri kwamiti na musamman, ta tura dokar zuwa gare su, domin su yi duba a kanta da kyau, su kuma fito da hanyoyin da idan anyi ta, za ta haifar da ɗa mai Ido.
