Ban taɓa zama ɗan jam’iyyar PDP ba – Akpabio

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Godswill Akpabio, ya musanta cewa ya taba kasancewa mamba a jam’iyyar PDP.

Akpabio ya bayyana hakan ne a zaman majalisar na ranar Talata, yayin da Sanatoci ke tattauna ƙudirin girmama marigayi tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Ibrahim Idris.

Sanata Jibrin Isah, mai wakiltar Kogi ta Gabas, ne ya gabatar da kudirin, inda ya tuna cewa marigayi Ibrahim Idris ya kasance mamba a PDP.

Yayin gabatar da kudirin, Isah ya ce shi da Akpabio da sauran ‘yan siyasar lokacin duk sun kasance cikin PDP.

“Marigayi Ibrahim Idris ya kasance mamba a PDP; ni ina nan lokacin da kai ma kake nan, dukkanmu muna can,” inji Isah.

Sai dai Akpabio ya katse shi, inda ya musanta cewa ya taba kasancewa mamba a PDP.

“Ban taɓa kasancewa a PDP ba. Wataƙila ruhina yana can, amma zuciyata ba ta taba kasancewa can ba. A koyaushe ni mai ra’ayin ci gaba ne,” inji Akpabio.

Akpabio ya kasance Gwamnan Jihar Akwa Ibom daga 2007 zuwa 2015, sannan ya jagoranci ƙungiyar Gwamnonin PDP a lokacin.

An kuma zabe shi Sanata a shekarar 2015 a karkashin tutar PDP, inda ya rike mukamin Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattawa daga 2015 zuwa 2018.

Daga bisani, Akpabio ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a shekarar 2018.

By ukarofi

Leave a Reply