Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Oyo kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APM, Seyi Makinde, ya yi alkawarin sake fasalin Nijeriya cikin shekaru huɗu idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a shekarar 2027.
Makinde ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin taron masu ruwa da tsaki na yankin Arewa ta Tsakiya da tawagar yaƙin neman zaɓensa ta gudanar a Lafia, Jihar Nasarawa.
Ya ce shi mai son kawo sauyi ne, yana mai cewa idan aka zaɓe shi, zai yi amfani da wa’adin mulki guda wajen sake fasalin ƙasar.
Makinde ya ce shirin nasa zai mayar da hankali kan tsaro, ilimi, tattalin arziki da tsarin siyasa da zamantakewa, yana mai cewa za a iya kammala sauyin cikin wa’adi guda na shekaru huɗu.
Ya kuma ce idan ya zama shugaban ƙasa daga ranar 29 ga watan Mayun 2027, zai kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa ta wucin gadi wadda za ta samar da sabbin manufofi da sabbin hanyoyin bunƙasa Nijeriya.
Ya ce za a sake fasalin tsarin tsaron ƙasar, a inganta ilimi, tare da farfaɗo da tattalin arziki ta hanyar amfani da bayanai da dabarun zamani.
Da yake magana kan matsalolin tattalin arziki, Makinde ya ce sake fasalin tattalin arzikin Nijeriya zai taimaka wajen rage matsin rayuwa ga ’yan ƙasa baki ɗaya.
Ya kuma ce nasarar zaɓen 2027 ba za ta dogara da masu hannu da shuni ko kuɗin da ’yan siyasa za su kashe ba, sai dai ra’ayin al’ummar Nijeriya.
A ɓangaren tsaro kuwa, Makinde ya soki shirin Gwamnatin Tarayya na kafa sabbin rundunonin soji domin yaƙi da rashin tsaro, yana mai cewa bai ga tanadin kuɗin wannan shiri a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026 ba.
Ya ce gwamnati ba za ta iya ɗaukar irin wannan muhimmin mataki ba tare da tanadin kuɗi da cikakken tsari ba.
Makinde ya kuma ce duk da ƙarin kuɗaɗen da jihohi ke samu daga Asusun Tarayya, hakan bai warware matsalar yunwa da tsadar rayuwa ba, yana mai cewa Jihar Oyo ma ta ƙara dogaro da kuɗaɗen da take samu daga Gwamnatin Tarayya bayan cire tallafin man fetur.
